advanced Search
Dubawa
5142
Ranar Isar da Sako: 2019/06/15
Takaitacciyar Tambaya
idan mala’iku ne zasu taimaki imam mahdi (aj) su agaza, to dom me zai faku ba zai bayyana ba?
SWALI
ya zo a ruwaya cewa sanda aka haifi imam mahdi (aj) sai naga –inji mai ruwaya- wani haske ya keto sama ya mamaye sasanin sama. Sai naga wasu tsuntsaye farare suna sauka daga sama suna fukafikansu suna shafar fuskokinsu da daukacin jikinsu sannan sai su tashi sama. Sai muka fadawa baban muhammad sai ya yi murmushi. Sannan ya ce: “ai mala’ikun sama ne suke tabarruki da haifuwar wannan jaririn, sune mataimakansa idan ya bayyana” to idan mala’iku ne zasu taimaki imam mahdi (aj) su agaza, dom me zai faku, ba zai bayyana ba?
Amsa a Dunkule
Game da bada amsar tambayar tilas mu lura da abubuwa biyu:
Nafarko: Taimako na Ubangiji yana da sharuda na musamman. Idan sharudan basu kamalla ba to taikakon ba zai samu ba. Misali sharudan sun kammalu a yakin Badar sai tallafin Allah da taimakon Ubangiji suka samu ga musulmin kamar yadda
Alkur’ani Maigirma ya tabbatar. Sai dai an sami akasin hakan a yakin Uhdu.
Na biyu: Hikimar Fakuwa bata takaita bane ga jin tsoran fuskantar hadari ga rayuwar Imam; (AJ) akwai wasu dalilai da kikimomi da nufin jarabta ga muminai da kuma yin jarrabawa ga Bil Adama. Koda yake mu Shi’a mun yi ammanar cewa babbar hikimar fakuwar Imam, wani sirri ne daga cikin sirroka na Allah da ba za’a san su ba sai bayan bayyanarsa (AJ).
Amsa Dalla-dalla
 Malaman Shi’a sun bayyana cewa daga cikin hikimomin fakuwa Imam (AJ) harda kare rayuwarsa mai albarka daga fuskantar duk wani hadadari. Watakila hakanne ya jawo wannan tambayar. Ma’ana yaya za mu iya tara batun cewa rayuwarsa mai albarka da batun cewa Mala’iku suna mataimakansa kana masu tallafa masa?
Ko kuma a ce: To idan da taimakon Ubangiji don kare rayuwarsa, tomene ne dalilin fakuwatasa?
A nan tambayar ta na da dagantaka da fakuwa da kuma hikimar yinta; Bisa haka tilas mu mu yi nuni zuwa ga mas’aloli biyu:
Tafarko: Menene sharudan samun taimakon Allah?
Ta biyu: Menene muhimmin dalili na yin fakuwa? Shin ya takaita ne ga jin tsoro ga rayuwar Imam?
1. Taimakon Allah ya na da nasa tsarin
Bisa rashin la’akari da inganci ko rashin ingacin ruwayar ko ingancin matanin hadisin ba. Tilas a duba wani mahimman bayani wadda shi ne: Abinda za’a iya fahimta a wadannan ruwayoyi shi ne cewa bayyanar Imam Mahdi (AJ) bata takaita ga mujiza da wasu lamura da suka saba wa dabi’a kawai ba. A bangaren taikamakon Allah kuwa, ruwayoyi sun nuna cewa: “Idan Imam Mahdi ya bayyana wata tawaga ta mala’iku ce zata taimakesh shi da sahabbansa” [1].
Abin da ya kamata a fada anan shi ne, shi fa taimakon Allah na boyen kan gudana ne bisa tsari da tafarki na musamman. A cikin suratul ‘Ali’imrana aya ta 123-124 an yi tsokaci dangane da taimakon Ubangijin a yakin Badar: “Hakika Allah Ya taimaka muku a Badar kuna ‘yan tsiraru, to ku ji tsoran Allah ko zaku iya godiya* Yayin da Yake gaya wa muminai ashe bai ishe ku ba Allah Ya karfafeku da mala’iku dubu uku suna masu sassauka ba” [2].
Abin lura anan shi ne, ita aya da ta biyo bayan ayoyi biyun tana nuna cewa taimakon Allah kan samu ne bisa sharuda na hakuri da tsoron Allah.
Za’a iya tsamo wadannan sharudan ne daga ayoyin Alku’ani Maigirma daga ciki akwai fadin Allah (s.w.t): “Ya ku wadanda kuka yi imani in kun taimaki Allah to Shi ma zai taimake ku ya kuma tabbatar da digadigenku” [3]da sauransu, Daga wannan ayar abinda zamu fahimta shi ne, taimakon Allah ba kara-zube yake zuwa ba, ko kuma ba da wata kaidi ta musamman ba. Shin akwai wanda ya isa furta cewa idan mala’iku na taimako da agaji to me yasa basu taimaki mumina ba a yakin Uhudu har aka tarwatsasu?
An san cewar su muminai a yakin Uhudu basu bi umurni da aka bada hakan ya haifar da rashin taimakon Allah da tallafi na boye a garesu.
To hakan yake a tabangaren Imam Mahdi (AJ) babu wani bambanci da na muminan a zamanin fakuwa. Babu shakka wannan taimakon kan tabbata ne idan sharudan saukarsun suka cika. Daga cikin sharudan akwai samun jajirtattun mataimaka masu tsantseni kamar mataimakan Annabin Girma (s.a.w) a yakin Badar.
Ruwaya ta tabbatar da cewa idan Imami Ma’sumi ya sami mataimaka adadin na Badar, to wajibi ne ya yi yaki. Shaihin malami Mufid ya bayyana cewa “Lalle ne adadin da sifofin su zama tamkar na mayakan Badar har da karfin imani da iklasi” [4].
Bisa wannan idan aka samu adadin mayakan na Badar da kuma iklasi, to tilas Imam din ya bayyana. (matukar sauran sharudan suka cika da kuma yana yi da zamu yi bayaninsa a kasu na biyu) to da sannu sai mala’ikun su sauko don tallafawa da taimakawa ga muminan.
2. Tsoracewa rayuwar Imam ita ma tana daga cikikin hikimomim Allah kamar yadda malaman Shi. a suka ambaceata na tsoro ga rayuwar Imam (AJ), suka ce lamarinta babu bambanci da fakuwar Annabi a (s.a.w) (a kogon Sauru ko a kwarin Abutalib) don tsirar da kansa to hakanan fakuwa Imam[5].
Abin da yakamata a fada anan shi ne, Hikimar Gaiba bata takaita bane bisa jin tsoran fuskantar hadari ga rayuwar Imam (AJ) akwai wasu dalilai da kikimomi da nufin: 1-jarabta ga muminai da kuma yin jarrabawa ga Bil Adama. 2- kada ya zamana akwai mubayi’ar wani azzalumi a wuyansa (AJ) [6]. Bugu-da-kari mu Shi’a mun yi ammanar cewa babbar hikimar fakuwar Imam wani sirri ne daga cikin sirrori na Allah da jama’a ba za su santa ba sai bayan bayyanarsa (AJ) [7]. An ruwaito daga Imam Sadik (a.s) ya ce: (a.s). “Lalle ne ma’abucin wannan lamarin (Imam Mahdi) zai buya lilas duk wani batacce sai ya yi ta shakku”. Sai mai ruwayar ya ce: “Na zama fansa gareka, domme za’a yi buyar? Sai ya ce: “Bisa wani dalili da ba’a mana izini mu bayyana muku ba” Sai na ce: To me ce ce hikimar a buyarsan? Sai ya ce: “Hikimar ita ce irin hikimomin buyar wakilan Allah (s.w.t) da suka gabaceshi. Hikimar hakan ba zata fito ba sai bayan bayyanarsa (AJ), kamar yadda hikimar abinda Halluru (a.s) ya aikata na fuda jirgi da kisan yaro da tsai da Katanga ga Annabi Musa (a.s) sai lokacin da za su rabu”. Sannan Imam ya ce: “Ya Ibin Fadal, wannan lamarin lamura ne daga cikin lamuran Allah,kuma sirri ne daga Allah kuma gaibi ne na Allah” [8].
Anan zamu iya samun sakamako kamar haka; da farko: Taimakon Allah kan samu ne bisa sharudi na musamman; sai na biyu: Dalilin buyar Imami bata takaita bisa jin tsoro ga rayuwarsa ba har kuma a ce tun da ga mala’iku masu taimako da ba da kariya ba sai ya yi gaiba ba[9].
Don karin bayani duba:
  1. Littafin Al’adilla al-akaliya ala hayatil Imam (AJ), tambaya mai lambata 2420 ( ashafin yanar, 2940).
  2. Falsafatul dulu umrul Imam (AJ), a tambaya ta, 209 (lamba shafin Imam 1405).
  3. Almadulgaibi wa hifzu hayatil Imam (AJ), tambaya ta mai lamba 1426 (lamba shafin yanar gizo: 1437).
  4. Afa’ida’id min wujudi Imami (AJ) fi asril gaibati, lambar tambaya 6504 (lamar yanar gizo: 705).
 

[1] Allama Majlisi: biharun anwar: j 52, s 328, 361, 387.
[2] Aali imran: 123-124.
[3] Muhammad: 7.
[4] Mufid, risalatus salisa fil gaiba, aalaa aali Ja'afar, s 12, bugu na farko, mu’utamar na alfiyyar sheikh mufid.
[5] Sheik Tusi: algaiba, oga buzurg tehrani, s 61, maktabar Imam Sadik a najaf ashraf.
[6] Amini Ibrahim, Dodgustare Jehan, s 147, bugu na goma, intisharat shafak.
[7] Littafin da ya gabata: s 146.
[8] Allama majlisi, biharul anwar, j 52, s 91, daru ihya’ut turasul arabi, bairut.
[9] Karin bayani a duba falsafatu gaibatil Imam (aj), kibate bo gamhaye sabze intizar, intisharate khaniyye khirad.
 
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa