advanced Search
Dubawa
12601
Ranar Isar da Sako: 2012/05/05
Takaitacciyar Tambaya
Me ake nufi da Kalmar Rayuka, wadda ta zo a cikin Ziyarar Ashura? “Aminci ya Tabbata a gare ka ya Baban Abdullah da Rayukan da suka Sauka a Farfajiyarka”
SWALI
Me ake nufi da Kalmar Rayuka, wadda ta zo a cikin Ziyarar Ashura? Aminci ya Tabbata a gareka ya Baban Abdullah da Rawukan da suka Sauka a Farfajiyarka” Shin ana nufin Rawukan wadanda suke zuwa Ziyarar Imam ne? ko ana nufin Rawukan wadanda aka Bisine su a karbala kusa da shi? Ko Wadanda suka ba da Rayuwarsu ga Imam Husain, suka Sadaukar da Rayuwarsu a Hanyar Imam, (Sahabban Imam Husain)?
Amsa a Dunkule

 Abin da ake nufi da Kalmar ”Rawukan da suka sauka a Farfajiyarka” su ne Shahidai, wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai (A.s) a Filin Karbala.

Wadannan su ne Dalilan da suke Tabbatar da haka;

  1. A bisa Al’ada masu Ziyara wadanda suke da Rai ba a Kiransu da Sunan arwah. (Rayuka)
  2. Ita wannan Ziyara Zance ne daga wanda ya kawo Ziyara, a bisa Al’ada ba zai Zamo da mai Zance da wanda ake Zance da shi, a kira su da suna Daya ba.
  3. Dukkan Addu’o’in Ziyara da aka ruwaito ga Imam Husain (A.s) babu yin Sallama ga masu kai Ziyara Gare shi.
  4. An Ruwaito Ziyarar Ashura ne tun Kafin a Bisine Wadanda suke Kwance na yanzu a wurin, wannan ya nuna kenan, Kalmar Rayuka ba ta Nufin dukkan Wadanda suke Kwance a wurin.
  5. Daga cikin Kalmomin Shaidu da ke cikin wannan Ziyara zamu iya Fahimtar cewa Kalmar Rawukan Wadanda ake musu Sallama, su ne Shahidai wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai a Filin Karbala, domin yazo a cikin wani wurin, za’a yi Sallama ta Musamman ga Wadanda suke tare da Imam: (Amincin Allah ya Tabbata ga Husain da Ali Dan Husain da Yayan Husain da Sahabban Husain”

Kuma Kari aka haka shi ne cewa ai Ita Ziyarar Ashura, a Dunkule ta Kunshi yin Sallama ne ga Shugaban Shahidai da “ya” yansa da da Sahabbansa, da kuma bayyana so, da cika Alkawari ga Imam, da kuma Nesantar Makiyansa.

  1. Yazo a cikin wata Ziyara ta Ashura, Kalmar da take cewa: Amincin Allah ya Tabbata a gare ka da kuma Rawukan wadanda da suka sauka a Farfajiyarka, (Hallat da Anakhat) suka yi Jihadi don Allah a tare da kai, suka sayar da rawukansu don Neman Yardar Allah a cikin al” amarinka[1] Acikin wannan Jumlar wasu Suffofi sun Fito, irin su yin Jihadi a Hanyar Allah, tare da Shuigaban Shahidai (as) da yin Shahada don neman Yardar Allah tare da Shugaban Shahidai.Wadannan Siffofi sun zo ne bayan Siffanta su da Kalmar (Hallat da Anakhat) wato Sauka a Farfajiyar Shugaban Shahidai (as)

 daga wadannan Kalmomi za a Fahimci cewa[2] Kalmar Rayuka da a ke nufi shi ne Rawukan Shahidai Wadanda suke tare da Shugaban Shahidai.

  1. Yazo a cikin wata Addu’a ta Ziyarar Ashura, banda waccan da ta Shahara[3] Ana cewa: Amincin Allah ya Tabbata a gareka, ya Baban Abdullah Al Husain, da wadanda suka taimaka maka suka ba da taimako, suka Tayaka da Kawukan su, suka Mika Wuyayen su a wajen Kariya gareka, ….Aminci ya tabbata a gareka ya Shugaba na, (Aminci ) ya tabbata a gare su , da Ruhinka da Ruhinsu da Turbarka da Turbarsu , Aminci ya tabbata a gareka, ya dan Shugaban Halittu, da wadanda suka yi Shahada a Tare da kai.

 Daga wadan nan kalmomi za’a iya fahimta a fili cewa Kalmar rawukan da ake                    nufi su ne shahidan da suka yi shahada a tare da shugaban shahidai.

  1. Yazo a cikin wata Ziyara ta Shugaban Shahidai (as) Bayan an Karanta Ziyarar Imam Husain da Aliyyul Akbar (AS) sai a Fuskanci Shahidan Karbala a karanta wannan Ziyarar…….kuma Zamowar a cikin Dukkan Addu’o’in Ziyarori ga Shugaban Shahidai, babu yin Sallama ga masu Ziyara ko ga Wadanda aka Bisne su a wurin, zamu samu Natijar cewa abisa la’akari da Gamammiyar addu’o’in Ziyarori na Ashura da sauran Ziyarori na Shugaban Shahidai, ba tare da wani Kokwanto ba zamu iya cewa Kalmar Rawukan da ake Sallama a gare su Acikin Ziyarar Ashura su ne Shahidan da suke tare da Shgugaban Shahidai (as) (a lokacin shahadarsa).

 


[1] Sayyid Ibn Tawus, Ikbalul A’mal Juzu’i 3 Shafi-70

[2] Itace Ziyarar da take da irin Ladar Ziyarar Ashura, ga wanda ba zai iya yin dukkan Ladubban Ziyarar Ashura ba (na yin Kabbara da La’anta 100 da yin Sallama 100 da yin Sujuda da Sallah da yin Addua bayan ziyara) Mafatihul Jinan.

[3] Za’a iya Fahimtar hikimar Jinkirta Fadin Kalmar yin Jihadi da Shahada, sai bayan an Ambaci Kalmar (Hallat da Anakhat) Wadanda suke nufin Sauka, cewa Kalmar Rayuka na nufin Shahidan da suka yi Shahada a Ranar Ashura A tare da Shugaban Shahidai (as) .

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Mene ne Addini?
    11854 Hikimar Addini 2012/07/23
    An yi nuni da ra’ayoyi kala-kala masu yawa a addini kuma an yi amfani da Kalmar “addini” a wurare masu yawa da ma’anoni kamar haka: 1. Duk wani imani da wani karfi boyayye na gaskiya ne ko na barna. 2-kawai addinin Allah saukakke. Don haka ...
  • Yaya aka samu tunanin akidar Rashin addini mai cewa siyasa daban take da addini?
    7158 Sabon Kalam 2012/07/24
    A lokacin samun canjin turan kiristoci sun samu matsala da ta kai su ga cewa addini yana da tawaya, kuma ba zai iya biyan bukatun mutane sababbi ba a fagen siyasa da zaman tare, don haka sai suka kai ga tunanin raba addini da siyasa.
  • Shin a kwai wata madogara ta addini da ke nuna cewa turara kanyen esfand ko harmal na maganin riga kafi daga sharrin hassada?
    7558 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2017/05/20
    Ba zai yiwu ba ilimin da hankalin Dan Adam su riski wasu tabbatattun abubuwa ba, hassada ma na cikin waDancan abubuwan da hankali da ilimi basa iya tabbatarwa alal aKalla, hakama kuma hankali da ilimi basu samu dalilin kare hakan da watsi da shi ba. Idan muka ...
  • Mene ne feminism? (matuntaka)
    10579 زن و حکومت اسلامی 2012/09/16
    Feminism lafazin faransanci ne, kuma kalmace ta asalin yaran latin kamar haka ne ta zo da wani banbanci kadan a wasu yarukan kamar turanci da jamusanci, ana amfani da ita da wata ma'ana sananniya feminine, ma'ana ai mace (jinsin mace), femenism kamar wata kalma ce da ked ...
  • Mene ne ra’ayinku dangane da wilayar imamai ma’asumai (a.s) a kan mumini?
    6442 دانش، مقام و توانایی های معصومان 2012/07/25
    DAGA AYATULLAHI MUKARIMUSH SHiRAZY (MZ) ‘E’ imamai ma’asumai (a.s) suna da wilayar da Allah (s.w.t) ya sanya musu da wacce shari’a ta sanya musu duk gaba daya a kan muminai; sai dai cewa ita wilayar ta doru ne a kan wasu mas’lahohi wato wasu sharudda ...
  • A Wane lokaci tarihin musulunci ya fara?
    8217 تاريخ کلام 2019/06/16
    Bayan aiko Manzon Allah (s.a.w) zuwa lokacin da iyakancin zagayen fadin daular musulunci ta kasance a iyakancin wani yanki daga kasan saudiyya a yanzu, a sakamakon karancin adadin musulmai da kuma Karancin faruwar mihimman abubuwan (da za‘a ayi amfani da su a KirKiri tarihi), kari a kan ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    30776 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Zuwa wane haddi ne daula (gwamnati) ko doka zasu iya iyakance 'yancin mutum?
    8832 Tsare-tsare 2012/07/24
    Ana amfani da Kalmar 'yanci da ma'anoni daban-daban kamar zabi, barin 'yancin sha'awa da makamantansu, sai dai abin da yake ma'aunin bincikenmu a nan shi ne abin da ake gani a matsayin 'yancin dan Adam, ko kuma 'yancin al'umma a siyasance. Wasu mutane sun yi ...
  • Menene hukuncin miji da mata wadanda suke kallon fim din blue fim a tare?
    5688 2018/11/04
    an tambayi daftrorin marja’ai masu alfarma kan tambayar da ka yi kuma ga amsar da suka turo. Ofishin mai girma Ayatullah sayyid Ali Khamna’i (Allah ya tsawaita rayuwarsa): Kalllon finafinai masu tada sha’awa na sa mutun ya karkata zuwa tafarkin shedan na son zuciya kuma yana raunana ...
  • ya rayuwar Abuddarda” da kasance? mene ne Mahangar ahlul baiti a kan shi? Mine ne hukuncin ruwayoyin da a ka rawaito daga gare shi?
    9656 تاريخ بزرگان 2012/07/26
    {uwaimar dan malik} wanda ya shahara da alkunyar abuddarda”dan asalin kabilar khazraj yana daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.w). yana daya daga cikin mutanen khazjar da suke rayuwa a madina ya shiga musulunci bayan zuwan manzon Allah (s.a.w) madina da wasu yan watanni. Abuddarda”yana fifita imam Ali (a.s) a ...

Mafi Dubawa