advanced Search
Dubawa
18180
Ranar Isar da Sako: 2013/07/20
Takaitacciyar Tambaya
A ina ne za a iya yin salla da taimama maimakon wankan janaba?
SWALI
Saurayina da aka yi mana baiko yana yin wasa da ni wani lokaci da dare amma ba tare da ya shiga ciki ba... sai dai ba zai iya yin wanka don sallar asuba ba.! Shin zai iya taimama maimakon wankan janaba?.
Amsa a Dunkule
Idan dai mani ya fita daga gare shi ya samu janaba, to wanka ya zama wajibi kansa. Sai dai a wurare guda bakwai ne zai iya yin taimama maimakon wanka da suka hada da[1]:
  1. Idan ya zama ba shi da ruwa.
  2. Idan babu isasshen lokacin yin wanka ta yadda idan ya tsaya yin wanka to salla zata zama ramuwa.
  3. Idan ruwa zai cutar da shi ko kuma zai kara masa tsayin rashin lafiyarsa.
A nan zai iya yin taimama maimakon wanka. Amma idan saboda kunya ne ba zai iya yin wanka ba to ba zai iya yin taimama ba  a farkon lokaci don ya yi salla! Ya zama dole ne ya zuba ruwa a bangaren da ya zama najasa a jikinsa) kuma sai ya yi hakuri har zuwa karshen lokaci ta yadda zai iya yin taimama ya yi salla (da zai iya isar sa har ya yi salla ba tare da ta zama ramuwa ba), sai ya yi taimama ya yi salla yayin nan. Kuma jinkirta salla da kawar da damar yin wanka daga kansa da ya yi yana da zunubi don mu sani, ya yi sabo ke nan, sai dai duk da haka amma sallarsa ta yi[2].
 

[1] Taudhihul masa'il: hashiyar Imam khomain, j 2, sh 365.
[2] Taudhihul masa'il: hashiyar Imam khomain, j 1, sh 377, mas'ala: 679.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa