advanced Search
Dubawa
9153
Ranar Isar da Sako: 2016/07/12
Takaitacciyar Tambaya
menene cikakken tarihin rayuwar sahabi hujr dan Adi (rd) wanda kwanakin da suka wuce wahabiya suka aikata ta”addancin tone kabarinsa a kasar siriya?
SWALI
menene cikakken tarihin rayuwar sahabi hujr dan Adi (rd) wanda kwanakin da suka wuce wahabiya suka aikata ta”addancin tone kabarinsa a kasar siriya?
Amsa a Dunkule
Hujr bin Adi Al-kindi; ya na cikin sahabban manzon rahama {s.a.w} sannan bayan wafati ya kasance cikin kebantattun sahabban imam Ali (as) mai cika alkawali, hakika hujr bin adi ya halarci yakokin da imam Ali {as} ya jagoranta bayan wafatin manzon rahama ya kuma taimakawa imam da dukkanin karfinsa. bayan shahadar imam Ali {as} hakika hujr dan adi ya taka muhimmiyar rawa tsakankanin `yan shi”ar kufa ta yanda ya zamanto kayar makogaro ga yaran mu”awiya a wanda ya nada shuwagabanni a wannan yanki sakamakon ita kufa an mika ta hannun yaron mu”awiya zayad dan babansa, bayan matsanancin sabini tsakanin hujr bin adi da zayad dan babansa sai zayad ya sanya aka kama shi ya aika da shi wajen mu”awiya, yayin da aka kai shi sai mu”awiya ya nemi hujr da abokanensa  da su barrranta daga imam Ali {as} amma hujr da mutanensa sai suka yi watsi da wannan bukata ta mua”wiya wanda daga karshe ya sanya aka kasha su ta hanyar sare kawukansu.
 
Amsa Filla-Filla:
Hujr bin adi kindi;[1] galibin malamai masana tarihi sun kidaya shi cikin sahabban manzon Allah {s.a.w}[2] in banda yan tsiraru daga cikin malaman hadisin ahlus sunna da suka sanya shi cikin kason tabi”ai, wanda wannan sabani ya afku sakamakon wasu abubuwa kamar haka: ta kaka sahabi zai kashe sahabi wadanda dukkaninsu adalai ne a akidar ahlus sunna, sannan kuma ya za ai da adalcin mu”awiya gashi kuma ya kashe babban sahabi hujr bin adi kuma kebantaccen sahabin imam Ali {as} mai cika alkawali wanda ya halarci yakokin jamal da siffin da naharawan ya kuma kasance cikin kwamandoji.[3]
 
An baiwa imam Ali {as} labarin cewa hujr bin adi alkindi da amru bin hamakil kuza”I suna tsinewa mu”awiya a fili kuma suna zagin mutanen sham, sai imam Ali {as} ya aika musu da sako cewa su kauracewa aika hakan, yayin da su ka ji wannan labara sai suka je wajen imam Ali {as} su na masu tambayarsa: ya sarkin muminai ashe mu”awiya ba kan bata ya ke ba mu kuma muna kan shiriya? Sai imam ya ce:  ban son ace kun zama mutane masu yawan la”ance la”ance da zage zage. Kamata ya yi ku dinga cewa ya ubangiji ka kiyaye jinanen mu da nasu ka kuma sulhunta tsakanin mu ka shiryar da su daga batan da suke kai ta yadda duk wanda bai son gaskiya ba ya santa, wanda ke kan bata ya dawo shiriya.[4]
 
Yadda Aka Kama Hujr Dan Adi Da Yadda Ya Yi Shahada:
Daya daga cikin muhimmin abu cikin rayuwar hujr dan adi wanda tarihi ya fi mai da hankali kansa shi ne rawar da ya taka a cikin shi”an kufa lokacin shahadar imam Ali {as} hakika hujr dan Adi ya kasance babbar matsala ga yaran mu”awiya wanda ya nada su a kufa, hujr ya hana ya tsaya kyam ta yanda ya takawa madandanu da surutan Ziyad birki. Zayad ya tafi basara ya nada amru dan haris a kufa sai dai cewa labara ya isa kunnen zayad cewa hujr dan Adi da mutanensa sun yi taro suna barranta da la”antar mu”awiya a fili a bayyane sun kuma jejjefi amru dan haris sai take zayad dan babansa ya tafi kufa ya tara jama”a ya na musu bayani a dai dai lokacin da shi kuma hujr dan Adi na zaune ya kasa kunne ya na saurare har lokcin da ya ji zayad na yi masa barazana ya na cewa idan na samu damar mallakar kufa sai na sanya hujr bin Adi ya zama wa”azi ga ragowar mutane, sai zayad ya sanya aka kawo masa hujr dan Adi shi ko hujr na zaune bai ce masa komai ba, bayan an ja-in-ja da kuma fafatawa sai hujr ya yanke shawarar sulhu da kuma karbar aminci daga zayad don gudun kada su kashe shi, sai suka kama shi suka kai shi wajen mu”awiya, to a nan ne da yawan mutane wadanda cikinsu akwai munzir dan zubairu da umar dan sa”adu dan abi wakas suka ba da shaidar cewar hujr ya tara mutane suna zagin mu”awiya da la”antarsa ya na kuma kiransu da yakar mu”awiya da nuna musu cewa al”amura ba za su taba daidaito ba har sai dan dangin gidan Aliyu dan abi dalib {as} ya hau mulki, sannan kuma suka ce wai shi hujr ya koro gwamnan mu”awiya daga kufa sannan shi ya na ganin an zalunci imam Ali {as} ya na kuma yiwa imam din addu”a da nema masa rahamar ubangiji yana kuma barranta da dukkanin makiyansa da wadanda su ka yake shi.
Daga karshe dai mu”awiya ya nemi hujr dan adi da mutanensa su barranta kawukansu daga wilayar imam Ali {as} sai dai cewa ba su amsa wannan bukata ta mu”awiya ba, sai su ka yi ta yin salloli har zuwa wayewar gari. Bayan da gari yaw aye sai mutanen mu”awiya suka tafi da hujr makasa sai hujr ya yi alwala ya tsaya ya yi sallah bayan ya idar da sallah sai ya ce: idan lamarin ya kasance sabanin abin da ku ke tsammani cewa ina tsoron mutuwa ne to da zan yi salloli da yawa. Ina neman tsarinka daga wannan jarrabawa mutanen kufa na mummunar shaida kan mu, mutanen sham na kashe mu to a dai dai wannan lokaci sai Hadabatu dan fayyaz ya zare takobi ya nufi hujr dan adi sai hujr ya kama kyarma. Sai fayyaz ya cewa hujr kai da kake tsammanin baka tsoron mutuwa to idan haka ne ka barranta daga masoyinka ali ni kuma sai in kyale ka. Sai hujr ya ce masa: ta kaka ba zan ji tsoro ba alhalin ina tsaye tsakanin takobi da likkafani da kabari. Na rantse da Allah duk da cewa ina tsoron mutuwa sai dai cewa har abada ba zan furta Kalmar da za ta fusata ubangiji ba sai suka kashe shi.[5]
 
Dole ne mu lura da wani abu mai matukar muhimmanci; shi ne cikin masana tarihi an samu ittifaki kan kasantuwar mu”awiya ya ba da umarni kashe hujr ibn Adi a shekara ta 51 bayan hiiba.[6]
 Hujr ibn adi ya yi wasiyya kamar haka: kada ko wanke jinin da aka kashe ni daga jikina, ka da ku kwance sasarin da aka daureni, ku binne ni tare da rigar jikina, a haka zamu hadu da mu”awiya ranar kiyama.[7]
Dalilin kashe hujr ibn adi ya jawo wa mu”awiya martani da zarge zarge masu tsanani, da yawan masadir din da suka kawo tattaunawar a”isha da mu”awiya sun kawo cewa ita a”isha ta zargi mu”awiya kan kisan hujr ibn adi.[8] haka cikin tattaunawar mu”awiya da imam Hassan {as} ya tozarta mu”awiya kan wannan kisa na hujr ibn adi.[9]
 

[1] Dabakatul kubra li ibni sa’ad j6 shafi 241.
[2] Dabakatul kubra li ibni sa’ad j6 shafi 242.
[3] Usudul gaba juz 1 sh 261.
[4] Akhbarul diwal sh 165.
[5] Diwanil mabda wal khabar fi tarikh arab wal barbar. Tarikh ibn kaldun juz sh 15
[6] 2Tarih khalfati ibn kayyad sh 131.  Almusannaf juz 2 sh 54
[7] Almusannaf fi ahadis wal asar juz 2 sh 457
[8] Al”isti”ab juz 1 sh 330
[9] Nuzhatul nazir fi jam”I baina ashbah wanna”za”ir sh 82. Al”ihtijaj juz 2 sh 297
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menene hakikanin ma’anar salla?
    36439 Halayen Aiki 2012/07/25
    Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    7110 Tsare-tsare 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
  • Shin zai yiwu ai mana bayanin tafsirin suratu kausar?
    15332 Tafsiri 2017/06/17
    Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
  • Ta yaya za a magance matsala, idan lamarin na hankali ya ci karon da na addini?
    14504 Sabon Kalam 2012/09/16
    Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
  • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
    15739 تاريخ بزرگان 2012/07/25
    Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
  • Yaya aka samu sauyi a addinin Kiristanci, kuma da wane dalili ne ya samu karkacewa da jirkicewa
    12699 Sabon Kalam 2012/07/23
    Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
  • An lura da cewa Kur’ani mai girma shi ne mu’ujizar cika makin Manazannin Allah, to meye fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da ke akwai a cikinsa?
    16211 Ilimin Kur'ani 2012/07/25
    An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
  • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
    18045 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
    Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
  • Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
    40482 Halayen Aiki 2017/05/21
    Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    13746 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...

Mafi Dubawa