advanced Search
Dubawa
10746
Ranar Isar da Sako: 2012/07/24
Takaitacciyar Tambaya
Shin mutum zai iya dawwama; idan haka ne, don me ya sa bai dawwama ba a duniya?
SWALI
Shin mutum zai iya dawwama; idan haka ne, don me ya sa bai dawwama ba a duniya?
Amsa a Dunkule

Yana daga abin da yake jan hankli mai kyau a cikin kur’ani mai girma cewa yana ganin mutum wani halitta ne na sama madaukaki mai ‘yanci, kuma wannan jikin nasa ba komai ba ne sai wata sheka ta dan wani lokaci da ruhinsa ya fake a ciki domin ya samu wucewa daga wannan duniya ta jiki, zuwa ga duniyar dawwama. Shi mutum a halittarsa shi samamme ne da yake bukatar dawwama yake gudu daga gushewa da karewa, don haka mutum yana da janibobi biyu ne da ya hada da rayinsa wacce take bangare ne nasa na hankali da tunani. Da kuma jiki wanda yake wata wasila ce domin yin aikin ruhi (wanda yake daga duniyar sama) domin ya yi aiki a wannan duniyar da cikin wannan jikin. Amma jiki shi daman dan wannan duniyar ne da yake da siffofin jiki kamar launi da shakali da girma da karuwa.

Sannan daga cikin dalilan da suka gabata domin tabbatar da cewa ruhin mutum ba mai dawwama ba ne, zamu ga cewa duk sa’adda rayuwar mutum ta tsawaita ya wuce cikin rayuwa tun daga rayuwa zuwa samartaka sannan sai girma sai kuma tsufa, zamu ga jiki yana tafiya zuwa ga yin rauni da sakin dukkan gabobin jiki, yayin da zamu ga ruhi yana da akasin haka ne, domin shi yana wucewa marhalolin ne zuwa ga kamala da karfi da daukaka. Wannan kuwa duk yana nuni da cewa ruhin mutum wani abu ne daban ba jikinsa ba, kuma da haka ne zamu ga ubangiji madaukaki yana karfafa cewa mutum halitta ce mai dawwama, kuma wannan duniya ba zata iya yalwatarsa ba, kuma dawwamarsa tana iya samuwa ne ta hanyar samun aibn da yake wurin Allah da biyayyarsa, da bin umarninsa da dokokinsa.

Daga karshe zamu ga cewa tun da duniya gidan wucewa ne, kuma duniyar jiki ce mai karewa, to ba zai yiwu a yi maganar dawwama a cikinta ba, kuma tun da ruhin mutum shi samuwa ce ‘yar sama wace take saman zamani, to zai iya neman dawwama ta har abada, sai dai ba zai iya neman dawwama ba sai a lahira.

Amsa Dalla-dalla

Gaskiya ne cewa mutum yana kama da wani littafi wanda yake cike da sirri da fomuloli wadanda ba mai iya warware su sai wanda ya sannafa shi wanda shi ne mai kago halitta, wanda yake shi ne Allah madaukaki, domin shi madaukaki shi ne mai rubuta wannan littafin, mai magana da kalmominsa, kuma Allah ya bayyana hakikar wannan mutum, ya yi sharhinsa a harshen annabawa da waliyyai da mala’iku, yana mai nuna mafarin mutum da hanyar da ya bi da hadafin sa yake gabansa, yana mai nuni ga mutum, da sanar da kansa, da mahaliccinsa, da farkonsa da zamaninsa da gabansa, kuma idan ba a bar mahalicccin mutum ya dauki nauyin yin bayaninsa ba da yin sharhin hakikaninsa ba, da warware fomulolinsa ba, to babu makawa wasu zasu yi wannan aikin da sunan cewa su ma sun san mutum.

Sai ya koma kamar littattafan da aka saukar da suka gabata, sai a gurbata shi a canja shi, a fassara shi da dukkan ra’ayi, a boye hakikanin gaskiyar sirrinsa, a karkatar da shi daidai yadda son rai yake, da bin bukatu da kwadayin rai, kuma lallai wadannan manyan lamurra ne guda uku masu girma a gurbata mutum, a bayanin hakikanin waye mutum. Daga cikin abu masu muhimmanci wurin sanin hakikanin mutam ta fuskacin mahangar kur’ani yayin da ya yi warwara ga mas’alar mafarar mutum da makomarsa, shin ita mafarar da makomar jiki na kasa kawai da zai kare yayin da ya kare, kuma duk wani abu da ba jiki ba babu shi karya ne, ko kuma shi mutum wata halitta ce mai daraja ta sama, kuma wata rana zai bar wannan shekar ta jiki wacce aka tsare shi cikinta domin ya tashi ya koma zuwa ga duniyar yalwa da walwala mai fadi, domin jiki ba komai ba ne sai wani wuri da ya zauna domin ya samu ya wuce zuwa ga duniyar sama.

Kur’ani mai girma ya amsa wannan tambaya yana mai karfafa ra’ayi na biyu yana mai nuna farko da makomar mutum, da yanzunsa da nan gabansa, da makomar lamarinsa[1]. Kamar yadda ya bayyana tafiyar mutum da motsinsa zuwa ga dawwama ta har abada, da gudunsa daga halittar karewa, da tsoronsa daga iyaka da dabaibayi.

 

Rayi halitta ce ta sama (ta malakut)

Ruhin mutum shi wani isdilahi ne na Falsafa da ake gaya wa samuwar mutum da ba ta jiki ba, kuma yana koma wa zuwa ga kalmar kur’ani mai daraja ta lamarin Allah yayin da madaukaki yake cewa: “Lallai halitta da lamari nasa ne…”[2]. Kuma a wannan isdilahin akwai wani sirri mai girma da yake nuni da lamarin Allah da yake kunshe da kadaituwa da haduwa. Madaukaki yana cewa: “Lamarinmu ba komai ba ne, sai guda daya kamar kiftawar gani” [3].

A wannan duniya dole ne a samu girma da gwargwado musamman a wannan duniyar ta halittar jiki, hada da abin da yake faruwa na yanayin yawaituwa da yanayi, sannan yin yawa yana daga sha’anonin wannan duniyar ta halittun jiki, amma rai, shi yana daga duniya da take ba ta jiki ba, don haka ne ba ta da hukunce-hukuncen jiki, da siffofinsa kamar launi, da grima, da yanayi, da daduwa, da tsawo, da fadi, da zurfi, da shakali[4].  

 

Asali ruhi ne, jiki reshe ne

Hakikanin samuwar kowane mutum da ruhinsa ne, amma jiki shi wata wasila ce da take karkashin ikon ruhi, kuma wannan ba ya kore cewa mutum yana da jiki da yake tare da shi a dukkan duniyoyin da yake samuwa da ya hada tun daga wannan duniya, zuwa duniyar barzahu, da duniyar lahira, don haka kamar yadda jiki yake bin ruhi a wannan duniya haka nan ma yake bin jiki a duniyar barzahu da ta ranar lahira a alkiyama. Kuma kur’ani ya yi nuni da hakan yayin da yake jingina reshe zuwa ga kasa, kuma asali zuwa Allah madaukaki kamar yadda ya zo a fadinsa: “… Ka ce Ruhi yana daga lamarin ubangijina”([5])([6]).

 

Daidaituwar halittar runi

Allah ya halicci mutum mai daidaituwar halitta, kuma zai yiwu mutum ya kasance mai tawayar halitta a jiki sai dai wannan ba muhimmi ba ne kwarai, kuma duk sa’adda mutum ya samu tawayar jiki, sai nauyin takalifin da Allah yake dora masa ya ragu daidai gwargwadon tawayar wannan gabar, sai dai Allah bai taba halittar ruhi mai tawayar halitta ba har abada, hakika kur’ani ya yi ishara zuwa ga wannan lamarin yayain da yake cewa: “Da rai da abin ya daidaita ta” [7].

Sannan ya bayyana abin da ake nufi da daidaituwa a wannan ayar da cewa ya kimsa mata fajircinta da takawarta, domin rai din mutum, domin ran mutum abu ne wanda ba a riskarsa, don haka daidaituwarsa ya kamata ya yi daidai da ruhin sai ya kasance shi ma ba jiki ba ne, don haka ne ya ce: “Sai ya kimsa mata fajircinta da takawarta” [8]. Wato ya sanya mata sanin me ye fajirci, da kuma me ye takawa wadanda zasu sanya daidaito ga ruhi[9].

Ruhi ba jiki ba ne

Abubuwa sun kasu zuwa ga masu jiki da wadanda ba masu jiki ba, kuma dukkaninsu suna da siffofinsu na musamman, masu jiki suna siffantuwa da shakali da girma da launi da nauyi…, yayin da su kuma marasa jiki ba su da zamani da wuri, kuma ba su da shakali da girma da nauyi da lauini, kuma da yake babu tsakatsaki tsakanin masu jiki da marasa jikik, to idan ya tabbata cewa abu ba shi da jiki da siffofin jiki to babu makawa yayin nan cewa shi abu ne maras jiki.

Daga cikin dalilan da malaman Falsafa suka kawo don tabbatar da cewa rai ba jiki ba ce, to zamu wadatu da kawo dalili daya wanda yake shi ne tabbatar rai a dawwamar canje-canje.

Duk sa’adda mutum ya fuskantu zuwa ga tsufa da girman shekaru sai ka samu jikinsa da gabobinsa yana gangarawa zuwa ga rauni da canji, sai dai wannan janibin ruhin yana fuskanta ne zuwa ga akasain hakan, yayin da zamu ga yana da karkata zuwa ga kamala da daukaka a hankali da tunani. Wannan ba komai yake nunawa ba, sai cewa ruhi ba jiki ba ce da cewa wata aba ce mai zaman kanta daga samuwar jiki[10].

Mutum da dawwama

Idan muka samu mutum yana mai samun nutsuwa da rayuwar duniya, to wannan ba komai ba ne sai natijar sakamakon bangaren tunanin mariskai na jiki, kuma tun da mariskansa suna kusa da jiki ne, kuma hankali da mariskansa duk sun nisanta daga garesu, don haka ne sai muka samu mutum yana karkata zuwa ga abubuwan da suke na mariskan jiki masu jan hankalin mutum zuwa garesu.

Amma mutum mai hankali shi ba ya ganin wanta kima ga abubuwan da suke na mariskan jiki, kuma irin wannan mtumin ba ya fadawa cikin yaudarar duniya da rude-rudenta.

To mutum halitta ne shi mai karkata zuwa ga dawwama, kamar yadda Sadrul Muta’allihin yake cewa: Allah ya halicci mutum da fidirar son wanzuwa da kin karewa[11]. Don haka jin dadin duniya mai karewa ba ya iya kosar da shi, kuma idan ya karkata zuwa ga duniya to ta fuskacin kuskure ne, ko kuma yana mai mantawa cewa shi mai dawwama ne bayan mutuwa, ko kuma don ya samu jarrabawa ce da bala’in jahilci murakkabi, ko gafala, kuma nassin kur’ani yana cewa: “Dukkan rai mai dandanar mutuwa ce” [12], don haka dawwama a duniya wani abu ne mustahili da ba zai yiwu ba.

Don haka ne ubangiji madaukaki yake karfafar cewa mutum shi halitta ne mai dawwama, kuma wannan duniyar ba ta dace da dawwama ba, domin dawwama tana tare da samun abin da yake wurin Allah da tsantsar biyayya gareshi madaukaki, Ubangiji madaukaki yana cewa: “Abin da yake gunku yana karewa, abin da yake gun Allah shi ne mai karewa, kuma lallai za a saka wa wadannan da suka yi juriya da ladansu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa[13]. Kada ku daidaita dawwamarku, hakika ruwan rayuwa yana gun Allah madaukaki kawai, ba zaku iya samun sa wurin waninsa ba[14].

 


[1] Jawadi Amuli: Surat ba Sirate insani dar Kur’an: shafi: 35, 37.

[2] Surar A’araf: 54.

[3] Surar Kamar: 50.

[4] Hasan Zadeh Amuli; Fususul Hikam bar Nususul Hikam: Fas 31, shafi 179.

[5] Surar Isra’i: 85.

[6] Jawadi Amuli; Zan dar ayine jalal ba jamal, shafi: 68.

[7] Surar Shams: 7.

[8] Surar Shams: 8.

[9] Jawadi Amuli: Karamat dar Kur’an; shafi: 33.

[10] Hasan zadeh Amuli Hasan; Ma’arifate Nafs dafare Dubbun, shafi: 176.

[11] Sadrul Muta’allihin; Al’asfar j 4, shafi: 163.

[12]  Surar Aali Imran: 185.

[13]  Surar Naml: 96.

[14]  Jawadi Amuli: Karamat dar Kur’an, shafi: 116.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa