advanced Search
Dubawa
18613
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Ni saurayi ne kuma a yanzu ina da bukatuwar in san mene ne rayuwa da hadafinta.
SWALI
Ni Saurayi Ne Kuma A Yanzu Ina Da Bukatar Sanin Ita Kanta Wannan Rayuwar da kuma hadafinta. Na taba tattunawa da wasu dalibai, game da dalilin da hadafi na da rayuwa. da yadda ya wajaba rayuwar musulmi ta kasance. Sai suka ce dani ba makawa dole ne ayi koyi da daya daga cikin Imamai (a.s) a matsayin abin koyi a cikin rayuwa. To, ni a lokacin da na riki Imam Ali (a.s) a matsayin abin koyi a rayuwata na wani zamani mai tsawo, na fuskanci wasu tufka da warwara a cikin wasu kalamunsa na a cikin cikin littafin Nahajul Balaga. Misali yana fada a cikin daya daga cikin zantukansa na hikima: ” Mumini ya na da lokuta guda uku: lokacin da yake ganawa da Ubangijinsa, da lokacin da yake neman abincinsa da lokacin da yake kebanta tsakaninsa da ransa a cikin jin dadi na halaliya da kyawu” A cikin wannan hikimar, ba a ambaci wasu abubuwa daban ba, kamar neman ilmi da waninsa. don Allah ina Ina rokon a nuna mun hanya, a shiryar da ni zuwa ga hanyar da zata sa wa rayuwa ta hadafi na musamman, da ingantacciyar alkibla, wacce zanbi ta cikinta don isa ga martabar “mutum Kamili”.
Amsa a Dunkule

Akwai nassoshi masu yawa da suka zo a cikin koyarwa da dokokin musulunci wadanda suke nuni da hadafin rayuwa da cikakkiyar manufarta. shi Kur’ani Mai girma yana daukar cewa manufar rayuwa ita ce: “bautar Allah madaukakin Sarki, wadda ta hanyarta ce za a iya isa ga kamaloli na ruhi da samun arzikin duniya da lahira. A wani guri kuma yana nuni cewa manfuar rayuwa shi ne “rige-rige zuwa ga alhairai”. Akwai kuma Isharori masu zurfi, iyakantattu, a cikin ruwayoyinmu da ke nuni da rassan hadafin rayuwa. Game kuma da ciro hikimomi daga maganganun ma’asumai (a.s) da kuma fa’idantuwa da shi, dole ne mu fuskanci wadansu muhimman al’amura. shi ne cewa duk da cewa zantukansu (a.s). masu saukin fahimta ne ga kowa. sai dai idan muka yi nufin mu danganta musu wata magana, to dole ne mu kiyaye wasu sharudda da za mu ambata a cikin amsoshi na filla filla.

Amsa Dalla-dalla

Akwai isharori masu yawa a cikin shari’o’in musulunci da koyarwarsa game da hadafin rayuwa. Al-kur’ani mai girma yana nuni da cewa manufar rayuwa shi ne “bautar Allah madaukakin Sarki wanda ta hanyarta ce za a samu damar isa zuwa ga kamala ta ruhi da arzikin duniya da lahira[1].

Haka kuma Al-kur’ania ya yi ishara da wani hadafin kuma wanda shi ne yin rige-rige (tsakanin mutane) zuwa ga kyawawan aiyyuka da alherai[2].

Don samun karin bayani mai fadi sai a koma littafin sharhin Nahajul-Balaga wallafar Allama Al-Ja’afari cikin Mujalladi na 1, 6, da na 8. Da littafin “Takamulul-Insan al-ijtima’i” wallafar Shahid Mutadahhari (KS). kuma Akwai irin wadan nan amsoshin a cikin wannan dandalin. [3]

Kuma ya dace ayi la’akari da wasu ruwayoyi a wannan fagen.

A cikin ruwayar Imamus-Sadik (a.s) an ruwaito cewa: “Imam Husain bin Ali (a.s) ya fito a wata rana cikin sahabbansa, sai ya ce dasu: ”yaku mutane hakika Allah, wanda ambaton say a daukaka, bai halicci bayi ba face sai don su sanshi. Idan suka sanshi zasu bauta masa. Idan suka bauta masa zasu wadatu da bautar sag a barin bautar waninsa. [4]

Amma bincike na asasi wanda ya wajaba a fayyace shi, hanyar da za mu bi wajen fitarwa da amfanuwa da maganganun Imamai (a.s).

A cikin wannan mas’ala dole ne mu yi la’akari da wadannan abubuwan; duk kuwa da cewa zantukan Imamai (a.s) kusan kowa na iya fahimtar ta, sai dai duk da hakana idan muna son mu jingina wata magana gare su ko wani zance, to, dole ne mu yi la’akari da wasu sharudda da ka’idoji kamar haka: -

  1. dole ne a bambance tsakanin maganarsu gamammiya (wato ta gaba daya) da kuma kebantacciya. Yana yuwuwa su fadi magana gamammiya amma kebantacciya ga wanda ya fada ko ga wani daga cikin sauran Imaman (a.s).

Ashe ke nan akwai bukatar iya tattarawa da kuma cikakkiyar fahimta.

Misali idan muna son mu san ra’ayinsu (a.s) game da abin da ya shafi duniya da hadafin rayuwa, kuma mu iya danganta abin da muka fahimta din da musulunci, to ba makawa dole ne ya zomo mun nsan dukkan taskokin maganganun imaman, da cikakkiyar fahimtar maganganun ta yanda za mu kai matsayin da za mu samu nitsuwar cewa maganganun gamammune da ba a kebance su ba.

  1. Dole ne mu kasance muna iya ware tsakanin sakakken zancensu daga kayyadadensu. A saboda haka ya wajaba a san cewa maganar Imam Ali (a.s) bai kasnce kayadadde a cikin wannan mauru’in.
  2. Hakannan zantukan imamai su na zuwa a matsayin kebantattce ga wani lokaci ayyananne na musamman. Kuma yana iya yiwuwa wasu imaman ne za su kebance wannan zamanin. wannan kuwa shi ake kiransa da sunan “Nasikh Wal-mansukh”saboda haka, idan muna son mu danganta wani al’amari ga a’imma (a.s) to, dole ne mu tabbatar muna ilimin“Nasikh Wal-mansukh” a cikin maganganunsu.
  3. Dolene kuma mu iya ware tsakanin jerin maganganunsu da martabobin jerin zantukansu (a.s). Wani lokaci zatukansu (a.s) na iya zama ga mutane gama-garine (wato kowa da kowa) masu fahimta irin ta al’ada.

A saboda haka wajibine a ware su daga maganar da ya yi su don ajin masu fahimta matsakaici, da na masu zurfin ilmi. Misali, an tambayi wasu daga cikin a’imma (a.s) cewa: “Shin Allah yana iya saka duniya da duk abin da ke cikinta ya dunkuleshi a cikin kwai, ba tare da kwan ya kara girma ba, kuma duniyar bata kan kance ba. Sai Imamai (a.s) suka ba su amsa mabambanta (wato kowa gwargwadon fahimtarsa da iliminsa). Misali wasu sun amsa da buga misali da ido wanda kankantansa bai kai na kwai ba to, amma hoton da yake shiga cikinsa babba ne sosasi a lokacin yin kallo, to amma wannan amsar ba cikakkiya bace ga wasu mutanen, a saboda haka aka yi sharhin maganar a wata amsa ta daban,, ta yanda aka mayar da al’amarin a matsayinwata mas’ala ta akida. [5] Abisa wannan zai yi wuya sosai ace an samu warwara a cikin zantuka, kamar irin maganganun da ke cikin littafin Nahjul Balagah, wanda malaman musulunci da wdanda da ma ban a musuluncin ba suka samu kayayyakin da suke mema ido rufe. [6]

Amma maganar ka game da neman ilimi, za mu ce maka: Idan ka koma “Babin ilimi da Jahilci” cikin littafin Al-kafi mai daraja, zai bayyana mana ra’ayin musulunci akan neman ilimi da muhimmancin sa. Don an ruwaito a cikin wannan babin cewar shi ilmi da aikata shi, ibadace. Kai shi ne ma mafi girman ibada, ashe ke nan kakkasawar da Imam Ali (a.s) ya yi, wanda ka ambata zai yiwu a hada su. A inda ya ce (a.s) “Ku raba lokutan ku, gida uku …. ”domin neman ilimi shi ma ibada ne, a ta bangare daya, Ya hada har da neman Ilmi, domin shi ma ibadace ta wani bangare, kuma abincin ruhi ne na ma’ana, a wani bangaren, bari mu kawo wani misali daga cikin wannan babin. Imam Yana cewa “Neman ilmi da aiki da shi, su ne kamalar addini. Ku saurara! Lalle neman ilimi shi yafi wajaba a kanku fiye da neman arziki”[7].

A karshe, muna sanar da ku cewa a cikin wadannan al’amura masu tsauri yana da muhimmanci na wajabci akan ku dinga saduwa da malaman Addini, wadanda suka shafe tsawon lokutan rayuwarsu, wajen darasin wadannan ilmummukan Ahlul baiti (a.s) madaukaka. Ya wajaba ku amfanu da rayuwar su, kuma ku sani akwai masu yawa suna yin kwanto don dana tarko ga samari, don su cafke su, su kai su zuwa ga wurin da suke so. Da hanyar da zata nisanta su daga barin bin Allah da bautarsa, wanda babu kyakkyawar karshe da kawo musu arzikin duniya da lahira a cikinta. Muna roka mu dacewa a wurin Allah.

 


[1] Suratuz zariyat, aya ta 56

[2] Suratu hud aya ta7, da suratul mulk, aya ta, 2

[3] Mauru’i:manufar yin halitta, tambaya ta 685 (lambar dandali, 732) mauru;inhadafin halittar mutum, tambaya ta 1108, (lambar dandali (1766) wani mauru’in:hadafin halittar mutum, tambaya ta 2319 (lambar dandali3022) wani mauru’in kuma shi ne:hadafin n halittar mutum da duniya tambaya ta 1052 (dandali mai lamba………. )

[4] Littafin ilalush shara’i’I wallafar sheikhus saduk, juzu’I na daya, shafi na 9.

[5] Littafin biharul anwar, na Muhammad takiy, almadrisiy, juzu’I na 4, shafi na 143.

[6] Littafin, ma’arifatu nahjul balagah, wallafar ayatollah, shahid mutahhariy, da littafin mukaddimatu nahajil balagah, shahin muftin misira, sheikh Muhammad abduh.

[7] Littafin al kafiy, na Muhammad bin ya’akub, juzu’i na 1, shafi na30.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Da”awar shi”a kan riddar sahabban mazon Allah {s.a.aw} bayan wafatinsa da wacce ma”ana sahabban su ka yi riddar? Shin wannan da”awa za ta iya karbuwa kuwa?.
    12161 Tsohon Kalam 2014/01/27
    samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
  • Mene ne ma'anar jagorancin malami?
    12834 Sabon Kalam 2012/07/24
    Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci. "Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu: 1- Wuraren da wanda ...
  • Shin mutum zai iya dawwama; idan haka ne, don me ya sa bai dawwama ba a duniya?
    11634 Sabon Kalam 2012/07/24
    Yana daga abin da yake jan hankli mai kyau a cikin kur’ani mai girma cewa yana ganin mutum wani halitta ne na sama madaukaki mai ‘yanci, kuma wannan jikin nasa ba komai ba ne sai wata sheka ta dan wani lokaci da ruhinsa ya fake a ciki ...
  • Menene hukuncin miji da mata wadanda suke kallon fim din blue fim a tare?
    6979 2018/11/04
    an tambayi daftrorin marja’ai masu alfarma kan tambayar da ka yi kuma ga amsar da suka turo. Ofishin mai girma Ayatullah sayyid Ali Khamna’i (Allah ya tsawaita rayuwarsa): Kalllon finafinai masu tada sha’awa na sa mutun ya karkata zuwa tafarkin shedan na son zuciya kuma yana raunana ...
  • WADAN NE BAITOCI NE ABBAS YAKE RERAWA A LOKACIN DA YA ZO DIBAN RUWA?
    11564 Sirar Manya 2012/07/26
    Mayaka yayin mubaraza a zamanin da su kan yi amfani da wani zaurance (don shaida juna ko ba da sako a tsakaninsu) don haka su kan rera baitotocin waka don samar da karfin gwiwa ga mutanensu da raunana abokan gaba. Imam (a.s) da mutanensa sun yi amfani ...
  • don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) amintacce?
    6189 تاريخ بزرگان 2019/06/12
    Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana ...
  • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
    14051 2019/06/16
    dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
  • Wasu irin hadisai ne suka zo a kan Hukuncin dan zina?
    14544 Dirayar Hadisi 2012/07/25
    Ruwayoyi na musulunci daga annabi (saw) sun yi magana da bayyana hukunce hukuncen dan zina, za mu kawo irin babobinsu Gadon dan zina;- Babin cewa dan zina, shi wanda ya yi zinar ba zai gaje shi ba, da ita mazinaciyar, ko wanda ...
  • Ta wace hanya za mu iya kare kanmu daga kanbun baka?
    26372 Tafsiri 2017/05/20
    Kanbun baka na da tasiri a ruhin mutun wanda babu wani dalili da za a iya kore samuwar sa da shi, ballantana ma an ga faruwar abubuwa masu yawa da suka tabbatar da samuwar kanbun baka ko maita. Marigayi shekh Abbas Kummi ya yi wasici da a ...
  • Shin zai iya yuwuwa a kai ga martabar ubangijintaka?
    8568 Irfanin Nazari 2012/07/25
    Makamin matsayin ubangijintaka yana da matakai da marhaloli mabambanta, kuma don a samu wannan amsar dole ne a ga dukkan martabobi da ma’anonin baki daya. Idan abin da ake nufi da kai wa matakin ubangijintaka shi ne zatin mutum ta canja da sauyawar abin halitta ya koma ...

Mafi Dubawa