advanced Search
Dubawa
11537
Ranar Isar da Sako: 2012/04/07
Takaitacciyar Tambaya
Wane ne za a yi la’akari da cewa har yanzu yana gwagwarmaya da shedan, kuma ta yaya?
SWALI
So tari shedanu da rundunoninsu na cikin mutane sukan kai hari ga me imani da Allah, har sai sun sanya shi ya yi ridda ya kafirce ya koma mushriki. Waye wannan muminin da ake la’akari da cewa shi ne wanda ke gwagwarmaya da shedanu har zuwa yanzu nan, ta yaya hakan ta yiwu gare shi?.
Amsa a Dunkule

Lalle shi shedan daidai gwargwardon yanda ya zo a cikin Kur’ani yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkanin ‘yan Adam face bayin Allah nan da aka tsarkake. Su wadanda aka tsarkake, su ne wadannan da suka kai ga manyan–manyan mukamomi ta yanda shedan ba zai taba samun wata kofar da zai isa gare su ba.

A nan muna bukatar wasu hanyoyi wadanda ba makawa, don samun kubuta a fagen fafatawar nan da shedan da rundunarsa, har mu iya yakar sa mu kuma yi nasara a kansa. Bari mu yi nuni ga wasu daga cikin su kamar haka:

Imani: Kur’ani yana la’akari da imani shi ne abu na farko kuma ginshiki domin dankwafe mamayar shedan.

Tawakkali: wani jigo daga cikin abubawan ake nasara a kan shedan da rundunoninsa shi ne tawakkali ga Allah tsarki ya tabbata a gare shi.

Tsari (isti’aza): shi ma’anarsa na nufin neman mafaka ga Allah madaukaki.

Ambaton Allah: domin shi ambaton Allah yana baiwa mutum basira kuma yana nesanta shi daga waswasi, ya kuma toshe kofofin da shedan ke bullowa ta cikinsu.

Tsoron Allah: samar da tabbatacciyar dabi’ar tsoron Allah da kuma inganta ta yana bude idanuwan zuciya a kan waswasin shedan, sannan kuma ya kare mutum daga afkawa cikin komar shedan.

Amsa Dalla-dalla

Lalle shi shedan daidai gwargwadon yanda ya zo cikin Kur’ani, yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkan yan Adam sai dai bayin Allah wadanda aka tsarkake. Yayin da shedan ya yi rantsuwa a kan cewa sai ya halakar da mutane baki dayan su, sai dai wadanda aka tsarkake ‘’Ya ce, Ya Ubangiji tun da dai ka halakar da ni, to wallahi zan kawata musu barna a bayan kasa, kuma sai na halakar da su baki daya (1). ko kuma fadar Kur’ani mai girma, Sai ya ce; na rantse da girman ka sai na halakar da su baki daya. (2) Amma su mukhlasun (3)’’ wanda aka tsarkake su gwargwadon abin da wannan ayoyin su ka ce sun kubuta daga kangin shedan. Wannan tabbaci ne wanda Kur’ani ya bayyana kamar yanda shedan ya yi ikirari. Kuma Kur’ani ma ya fada cewa: Lalle bayina ba ka da wani iko a kansu, ubangijinka ya isa ya zama me wakilci’’ (4)

Hanyoyin gwagwarmaya da shedansu ne wadanda suka kai ga manya-manyan mukamai ta yanda shedan bashi da wata kafa da zai bi zuwa gare su. A nan muna bukatar wasu hanyoyi wadanda ake matukar bukatarsu don cimma nasara a wannan kokawar da shedan. Muna samunsu za mu iya yakarsa mu kuma yi nasara a kansa. Bari mu kawo kadan daga cikin su: -

  1. Kur’ani mai girma yana daukar imani a matsayin tubali na farko domin dankwafe mamayar shedan. Kamar yanda ya ce: ‘Yan da al’amarin yake shi ne bashi da iko a kan wadanda suka yi imani.5
  2. Wani ginshikin kuma daga cikin ginshikai masu sa a yi nasara a kan shedan da rundunarsa shi ne tawakkali: Allah ya ce lallai ba shi da wani karfi a kan wadanda suka yi imani, kuma ga Allah kawai suke yin tawakkali’’6 don haka imani da Allah mai girma da daukaka da ayoyin sa na hana biyayya ga shedan da kuma yadda da hukuncinsa a kan mutum. Ba shi da iko a kan wanda ya yi garkuwa da garkuwar imani kuma ya yi tawakkali ga Allah. Amma mulkinsa yana kan wanda ya karbi jagonrancinsa ya kuma hada Allah da wani ‘’abin sani kawai shi ne ikonsa na kan masu jibintar al’amarinsa, wadanda suka zama masu shirka da shi Allah’7
  3. Neman tsari: ma’anar sa neman mafaka a wajen Allah (s). ita wannan mafaka wani lokacin tana iya zama ta dabi’a ko kuma ta shari’a. Idan muka tunkude abubuwan sharri na dabi’a neman tsari zai tabbata a gare mu wanda yake daga cikin mafaka na dabi’a na Allah (s) wannan na nufin dukkan tsare-tsare, da al’adun ubangiji wacce aka sanya a cikin tsarin hallita. Ta hanyar sababi da tasirin dabi’a. Kuma har-wala-yau in aka kare kai daga sharrin zuciya za a sami fa’ida daga mafakar shari’a. Kamar yanda Allah ya ambata a cikin surar (Nas’’ wanda yake nuni ga koyarwar Allah tabbataciya a shari’a mai tsarki bisa tsari irin na ikida da kuma salo irin na tarbiya ‘’idan wani dan tunani mara kyau ya same ka daga shedan to, ka nemi tsari daga Allah shi mai ji ne kuma masani’8 shi tauhidi yana hukunta wa mutum neman dauki daga Allah (s) don samun amfani da alheri ta hanyar fara ayyukansa da ambaton Allah. Kuma ya nemi daukinsa don tunkude cuta da sharri, ta hanyar fara ayyukan sa da cewa ‘’a’uzubillahi’’ saboda hakika babu mai tasirantuwa sai Allah shi kadai a dukkan duniya. Kamar yanda ya tabbata a cikin tauhidi.
  4. Ambaton Allah: shi ambaton Allah yana taimakawa dan Adam da basira, ya kuma nesanta shi daga waswasin shedan, ya kuma toshe kofar da shedan zai isa dagare shi. Allah ya ce lalle wadanda suka yi takawa idan wani abu daga shedan ya shafesu, sai su ankara (tunawa) sai ka ga har sun fadaka (10) imam Al-Sadik (as) ya ce: shaidan bai samun ikon sanyawa mutun wasiwasi face sai idan ya bijirewa ambaton Allah (swt) sai kuma ka ga har su fadaka (12).

‘’Ta’if’’ shi ne kewaya gefen abu, to kamar yan da waswasin shedan yake kewayewa a gefen ruhin dan Adam da tunaninsa ba kakkautawa don ta sami hanyar kutsawa cikinsa. To haka nan shedan ba zai iya yin wani tasiri ba a kan ruhi mai karfin imani da kuma takawa. Amma fa koyaushe yana nan yana dakon wata dama wacce ta dace da shi sai ya watsa wasu sashen soye-soyen rai, kamar sha’awa da fushi da hassada da ramuwar gayya, har sai ya samu ya kutsa cikin sa domin kawai ya batar da shi.

Wasu hanyoyin daban masu amfani don tunkude makircinn shedan su ne: ambaton ahlul-bayt (as) da kyautatawa masoyinsu. Da dagewa don kaiwa ga matsayin wadanda shedan bai iya cimmasu da sauransu.

Sakamakon wannan binciken; lalle kudurce samuwar Allah (swt) mai kariya ce kuma mai fadakarwa ce sosai, tana taimakon mutum ta kuma kare shi daga sabo da zunubi. Haka nan ma fadakuwa game da girman Allah da hikimarsa da juyar da al’amura ga zatinsa mai tsarki tana zaburtarwa ga ruhin bawa cikin fito-na-fito dinsa da shedan. Tare da cewa karfafa imani da tawakkali, da kuma takawa, gami da ambaton Allah ko da yaushe, da kuma zuwa da ayyukan da ke jawowa da korar shedan. A karshe neman tsari na hakika a lokacin da aka hadu da sharri da barna ta fuskacin shedan. Dukkan wadannan ana daukarsu a matsayin matakai masu tasiri da fa’ida wajen kare kai daga kutsowarsa.

Abu muhimmi da zamu fada a karshe shi ne duk abin da aka ambata, zai yiwu ya tabbata ta fuska mafi kammala ta hanyar yin tawassuli da ahlul-bayt (as) da kuma kulawa da su da fuskantarsu.

Maudu’ai masu alaka da hanyoyin da shedan ke kutsawa cikin mutum 987 (mauki: 1051

Manufofin da shirye-shiryen shedan, 1144 (mauki: 1777)

  1. Alhijr, 39
  2. Surar Sad, 82
  3. Mai yin lkhlasi shi ne wanda ya karkade ruhinsa daga kulli da algushu hna dabi’a, da kuma al’amuran dukiya, ya kuma tsarkake ransa daga duk abin da ba Allah, ya kuma cika shi da sonsa.
  4. Surar israi.65
  5. Surar nahl, 99
  6. Surar nahl, 99
  7. Surar nahl, 100
  8. Surar a’araf, 200
  9. Surar fussilat, 36
  10. Surar a’araf, 201
  11. Al Muhaddith-al-Nuriy, Mustadrak-al-Wasa’il, juz1 sahfi178, mu’assasatu alul bayt, kum. 1404 kamari; almajlisi Muhammad bakir, behar-al-anwar, juz72 shafi124 mu’assasat al-wafa, Beirut, 1404 kamari
  12. Al Amudi, al-Tamimiy, Abdulwahid, Gurat-al-hikan.wadurrar-al-kalim. Shaafi188, maktaabat-al-islamiy, kum.1366, shamsi.
  13. A’araf, 201

 

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Meye matsayin jagorancin malami a tsarin siyasar musulunci?
    8086 کلیات 2012/07/24
    A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance ...
  • Wadananne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani na wannan zamanin?
    6496 Ilimin Kur'ani 2019/06/16
    Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin tafsiran da suka gabata: ta bangaren amsa shibuhohi da warware tambayoyi da lamurran da suke kai- kaiwa a kasuwar tunani da kwakwalen mutane, bisa dogaro da tafarkin yin amfani da ...
  • mene ne ma’anar Takawa?
    17318 تقوی 2012/07/25
    Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    16001 معاد و قیامت 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin hadisin da ke cewa “duk wanda ya mutu ba shi da bai’ar imamin zamaninsa (Imaminsa) ya yi mutuwar jahiliyya” daga manzo (s.a.w) yake kuwa?
    9625 گوناگون 2012/07/26
    Bai’a na da bangarori biyu, mai bai’a (sauran mutane) da wanda ake yi wa bai’ar (wato su ne manzo (s.a.w) da imamai (a.s)). Tare da cewar manzo (s.a.w) shi ne hujja kuma shugaba, don haka shi za a yiw mubayi’a a matakin farko wato shi ne farkon ...
  • Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
    9278 2019/06/16
    Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
  • mene ne gwargwadon tasirin Allah madaukaki a rayuwar mutum?
    16378 Irfanin Nazari 2012/07/25
    Ba yadda za a wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima, wannan iradar ta Allah tana nan a ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, da dukkan dokokin rayuwa ba tare da ta cire wa mutum zabin da yake da shi ...
  • A zaben jagora malami ba kai tsaye ba akwai matsalar kai-kawo, to yaya za a warware wannan?
    7661 انتصاب یا انتخاب 2012/07/24
    A yanzu haka a jamhuriyyar musulunci ta Iran ana ayyana ‘yan takarar majalisar Khubrigan ta hannun shura Nigahban ne. To akwai batun sukan cewa Jagora shi ne yake ayyana ‘yan shura Nigahban, su kuma suke ayyanar cancantar shiga takara ga ‘yan majalisar khubrigan, su ‘yan majalisar khubrigan ...
  • yaya halittar mutum take a a mahangar musulunci?
    10480 Sabon Kalam 2012/07/23
    Ta mahangar Kur’ani mutum halitta ce da yake fizguwa zuwa ga ubangjinsa bisa fidirar halittarsa, kuma yake da jawuwa zuwa ga jiki, wannan halittar tana jansa zuwa ga ilimi da sani da alherai, a daya bangaren jiki tana kiransa zuwa ga sha’awa da sharri. Rayuwar mutum wani ...
  • Shin zan iya samun dama game da yin wani aikin na biyu bayan wanda nake yi
    7035 دنیا و زینتهای آن 2012/07/25
    Shari’a ba ta hana mutum yai koyi ko ya kware kan wata sana‘ar ba bayan wacce yake yi ko ya iya ko yin aiki sama da yadda ya saba abin kawai da shari’a ta hana kuma take kara tsoratarwa a kansa shi ne son duniya da nace ...

Mafi Dubawa