advanced Search
Dubawa
7772
Ranar Isar da Sako: 2014/08/01
Takaitacciyar Tambaya
Me ya sa Kur\'ani ya fifita yahudawa kan sauran mutane?
SWALI
Ya zo a wata aya a cikin surar Bakara cewa Yahudawa su ne mafifita, ya fassafar al’amarin ya ke?
Amsa a Dunkule
Allah madaukaki ya yi magana kan jikokin Annabi Yakub yana mai cewa {yaa bani isra’ila ....... inni fadhdhaltukum alal aalamin} {ya ku ‘ya’yan Yakub ....... hakika ni ne na fifita ku a  kan sauran mutane}. Tabbas wannan ayar ba ta magana kan yahudawan zamanin Manzo (s.a.w) da wadanda suka zo a bayan sa ba, sai dai tabbas tana magana kan mabiya annabawa kamar su Annabi isa da Musa (a.s) ne wadanda suke a zamanin wadannan annabawan wadanda aka kallafawa yin biyayya ga wadannan manzanni na ubangiji, kuma abin da ake nufi da fifilo kan mutanen duniya, ba yana nufun fifiko kan dukkanin mutane a tsahon tarihin Dan’adam a doron kasa ba, sai dai abin da ake kufi shi ne muminai yahudawa na zamanin da addini yahudawa ya zama shi ne hujja a wancen zamanin suna da fifiko kan sauran mutanen da suka rayu a iya takin wannan zamanin kadai.
 
Amsa Dalla-dalla
Dukkanin addinai Allah ta’ala a zamanin da suke ke ci su ne suka fi zama mafifita kuma mafi amintuwa zuwa ga hakika da rabauta. Don haka mabiya wannan addinin su ne wadada suka fi falala da fifiko kan dukkanin mutane. Ya zo a cikin wasu ayoyi na al’Kur'ani mai girma, Allah madaukiki ya siffanta banu isra’ila[1] da cewa: {ya ku (‘ya’yan Isra’ila) ‘ya’yan Yakub ku tuna ni’imomi na da na ba ku kuma hakika mun fifita ku a kan sauran mutane (mutanen zamaninku)}[2].
Kuma maganar wannan fifiko ta gudana a harshen Annabi Musa (a.s) ma: ≪(Annabi Musa ya sha mamaki tare da ban al’ajabi) sannan ya ce ashe yanzo kwa bauta wa wanin Allah (wanda ta ko ina bai cancacta a bauta masa ba) kuke so in rike shi a gare ku a matsayin abin wabta alhal (Allah) shi ne ya fifita ku a kan mutane (zamaninku) baki daya≫.[3]
A wannan ayar an kawa bayanan abubuwan da ake bukatar a sani. Na farko ayar ta yi nuni kan irin ni’imomin da ya yi musu. Na biyu kuma ta yi nuni kan abin da ake nufi da fificin da Allah ya yi musu. Wato da abin da ya fifita su. Da dai sauransu.
A nan zamu iya kawo wasu ayoyin da suka bada misalsalin kan no’imimin da Allah ta’ala ya yiwa yahudawa. ≪hakika mun bawa yahudawa littafi da hukuma da annabta kuma mun azurta su daga dadada kuma muka fifita su kan mutanen (zamaninsu)≫[4].
Allah ya yi wa yahudawa ni’imomi masu yawa daga cikin wadanna ni’imomin akwa shiryar da su da kuma yin imani har zuwa lokacin da suka kubuta daga tarkon fir’aunoni kuma suka dawo da girmansu da ‘yancinsu[5], sannan aka ciyar da su abinci daga sama[6], kuma lalle Kur'ani ya kawo kissoshi masu yawan kan ni’imonin da aka yiwa yahudawa masu yawan gaske.
Bisa haka ne wasu daga cikin mafassara suka cewa daya daga cikin baiwar da Allah ya yi wa yahudawa it ace samun Annabawa masu yawa a cikinsu[7] don bisa hakika samun mutane tsarkakakku masu yawan gaske a cikin al’umma ba karamin tasiri gare shi ba a cikin zurin wannan al’umma ta yadda hakan na sa masu imani da Allah su yawauita kuma wannan zai sa su fi sauran gungun mutanen fifiko.
Ta wani bangaren kuma idan fifikon banu isra’il da gamammiya ma’ana ce ta yadda ya hada har bayan lokacin Annabi isa (a.s) la’akari da cewa mafi yawan mabiyansa sun kasance daga cikin banu isra’il ne wadanda ake kira da ahlulkitabi (ma’abota littafi) to tabbas wannan ma’anar ba ta shifi lokacin bayan aiko Manzo (s.a.w) muhulunci ba har abda. Domin shi da al’ummarsa ba kawai sun fifici sauran al’umma ba ne, ballantana ma rashin yi masa biyayya na sa mutane su zama ababan zargi, kuma a takaice haka na sa mutum ya bar tafarkin gaskiya. Bisa wannan asasi falalar da ake managa a akai ta yahudawa ta kebanta da lokacin da ya gabata kadai.
La’akari da abin da ya gabata ya bayyana a sarari cewa, ayar nan da ke cewa ≪mun fifita su kan talikai≫ ba tana nufin dukkanin talikai a tsahon tarihi ba ne. ballantana ma abiin da take nuni shi ne fificin ‘ya’yan yakub (a.s) a zamanin da addinin yahudanci ya kasance shi ne hujja[8]. Kuma ba ta hada har da yahudawan da Kur'ani ya sauka a gabansu a lokacinsu ba. ≪shin ba na ba ku labarin wadanda suka fi kowa mummunan sakamako a wajen Allah ba, su ne wadanda Allah ya la’ance su ya yi fushi da su ya maida wasu daga cikin su burai da aladu kuma suka bautawa dakutu wadannan su ne mafi sharrin matsaya kuma sun fi kowa bacewa daga tafarki madaidaici≫[9].[10]
Akwai wasu karin dalilai kan rashin tabbatar wannan fifikon
Na daya. Akwai ayoyi da ke nuna cewa musulmai su ne mafifita al’umma da aka fitar daga cikin mutane baki daya kamar haka: {ku ne mafi alkahirin al’ummar da aka zaba daga cikin mutane.....}[11].
Na biyu. Tabbas yahudawa ba su da fifiko a kan ya’akuba da Ishaka da Ibrahim (a.s).
Na uku. A cikin Kur'ani ba kawai banu isra’ila aka ambata da cewa su ne suka fifici wasu ba, tabbas an ambaci fifikon wasu daidaikun mutane da kuma gungun mutane a matsayin wadanda suka fi kowa.
{hakika Allah ya zabi Adam da Nuhu da Ibrahim da Alayen Imrana (saboda cancantar da suka da ita) a kan talikai baki daya}[12].
{Haka ma (mun shiryar da) Isma’il da yasa’u da yunusa da ludu kuma dukkaninsu mun fifita su kan talikai}[13].
Don haka ida muka fassara wannan jimlar {mun fifita su a kan talikai} da ma’anar cewa suna da fifiko a kan kowa za a sami cin karo da juna da sauran ayoyin da suka gabata.
Daga karshe ya zama lalle mu lura da cewa mun wuce gona da iri sosai kan fifkon da zabin da ubangiji ya yi yahudawa, don haka ne ma muke ganin yadda Allah madaukaki yake magana kan kura-kuran su kuma yake zarginsu munanan ayuuka fiye da kowa a cikin Kur'ani mai girma.
 

[1] Ma’anar banu isra’ila a wannan ayar da ma ayoyi masu kamanceceniya da ita na nufi yahudawa.
[2] Surar bakara aya ta 47.
[3] Surar a’arafi a ya ta 140.
[4] Surar Jasiyati aya ta 16.
[5] Makarim Shirazi , nasir a cikin tafsirul amsal j1 shafi na 220, Tehran darul kutubul islamiyya bugu na daya 1374.
[6] Surar Bakara aya ta 57.
[7] Muhammad  Jawad mugniyya a cikin rafsirul kashif j1 sh 95 Tehran darul kutubul islamiyya bugu na daya 1424.
[8] Danrasi fadhlullahi bini Hasan a cikin tafsirin majma’ul bayan wanda balagi, Muhammad  Jawad ya yi wa gabatarwa j 1 sh 221. Tehran nasir khusru bugu na uku 1372. Da kuma inbi kasir damashki isma’il dan Amru a cikin tafsirul kur’an al-azim, wanda shamsuddin Muhammad  Husain ya yi wa tahkiki j 1 sh 158. Bugun bairut darul kutubul ilmiyya. Mabugar umuhammad Ali baidhun, bugu na daya, 1419. Da fakhrud dini alrazi muhamma dan umar a mafatihul gaibi j 3 sh 493. Bairut daru ihya’I turasul arabi bugu nauku 1420.
[9] Ma’da aya ta 60.
[10] Fakhrud dini alrazi muhamma dan umar a mafatihul gaibi j 3 sh 493. Bairut daru ihya’I turasul arabi bugu nauku 1420.
[11] Surar Ali Imran ku ne mafifita al’umma da aka zabo daga mutane.
[12] Ali Imran aya ta 33.
[13] An’ami aya ta 86.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa