Please Wait
8228
- Shiriki
Ma’aunin shiga aljannan shi ne imani da aiki na gari.
Dan shi’a ma zai shiga cikin aljanna bisa sharadi, kasantuwar sa dan shi’a kadai ba zai zama dalilin shigar sa allajannan ba, ya zama lallai ya yi aiki da abin da zai tabbatar da cewa shi dan shi’a ne, kuma lallai ya zama ya yi wa kansa tanadi don ya sami damar shiga cikin wadanda za a ceta.
Mabiya dukkanin wani addini na sama kafin wata shari’a sabuwa ta zo musu idan suka yi aiki da koyarwar addininsu to zasu shiga aljanna, sai dai bayan da aka aiko manzo Muhammad (s.a.w) kadai addinin da Allah Ta'ala ya yarda da shi shi ne addinin nusulunci na hakika wanda zaka same shi a a cikin makarantar Ahlul baiti (a.s).
Ko da yake idan amuka koma zuwa kar’ani da ruwayoyi zamu ga an ciro daga gare su cewa wandanda suke raunana. Raunana su ne mutanen da ba su da hanyar da zasu iya gano gaskiya ko kuma ba za su iya yin hijira zuwa kasashe don gano gaskiya ba, amma sun yi rayuwarsu bisa dabi’a ta dan ’adam to suma zasu sadu da rahamar ubangiji madaukaki. [i] wannan ya hada da raunana da jahilai da aka tauye da yaran da ba su balaga ba tare da mahaukata.
Kadai wadanda suka yi jayayya suka yi wa gaskiya taurin kai da ma wadanda su ka yi sakwa-sakwa tare da yin sakaci wajen sanin gaskiya ne masu laifi kuma ba zasu tsira ba. Amma mafi yawan mutane wadanda suke an tauye su ne kuma ba su yi taurin kai ba, zasu tsira cikin ludufin Allah Ta’ala da rahamarsa.
[i]Jigon da ke da alaka da: jahannam da wadadan ba musulmai ba, tambaya 47 (sait 283).
Ba a shiga aljanna da suna ko da yin da’awa, balle ma ita aljannan ana shigar ta ne ta hanyar imani da yin aiki na gari.[1] Saboda haka duk wanda ya yi riko da wadannan tsanikan guda biyu to ya bude wa kansa hanyar shiga aljanna a ranar tashin kiyama, in ba haka ba to ya kama hanyar wuta, sai dai in yana daga cikin raunana wadanda rahamar Allah mai yalwa ta lullunbe su, suka fada hannun ceton masu ceto, suka sami tsira daga azabar ubangiji.
Alkur’ani mai girma yana fadin kan haka:- {hakika wadada suna yi imani da wadanda suka bi addinin yahudanci da addnin nasaranci da addinin sabi’iyyanci dun wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira daga cikinsu kuma ya yi aiki na gari suna da sakamako a wajen ubangijinsu babu tsoro a tare da su kuma ba zasu yi bakin ciki ba}. [2]
Wannan ayar mai girma ba ta isu da kasancewar mutum bayahude wajen cancantar shigar sa aljanna ba har said a ta hada da imani da aiki na gari.
Daga nan ne zamu fahimci cewa kari a kan haka an sharadanta cewa wannan addinin ya zama ba a shafe shi da addinin da ya gabace shi ba, addinin annabi Musa (a.s) ya kasance shar’antaccen addini har zuwa kafin aiko annabi Isa (a.s), wa kazalioka addinin annabi isa (a.s) shi ma ya inganta a bauutawa Allah Ta'ala da shi har zuwa kafin aiko manzon rahama annabi Muhmnad (s.a.w). kafin a shafe shari’o’in da suka gabata.
Don haka yin da’awar cewa mutun shi mabiyin wani annabi ko addini ne bai isar ba, lallai ya zama dole a hada imani tare da lazimtar abin da imanin ya lazimta na akida na daga aikin kirki da halayya ta gari dss, domin imanin ba zai taba zama na gaskiya ba, sai mutum ta lazimci abubuwan dake tattare da imanin. Don haka abin da ya lazimci yin imani da annabi Musa shi ne karbar sakon da annabi ko annabawan da suka zo da shi a bayan sa, kuma abin da ya lazimci yin imani da annabi isa shi ne karbar sakon da ya zo daga mafifitan annabawa wanda ya zo a bayan sa. Wanda shi ne annabin da aka yi alkawarin zuwansa, a kan haka abin da ya lazimci yin biyayya ga mafifitan manzanni shi ne sallamawa umarninsa yanke take, da kuma abin da ya dora mutane a kai. Kuma daga cikin umarnin sa da abin daya dora mutane a kai akwai yin riko da halifanci imam Ali (a.s) da ‘ya’yanyen sa guda goma sha daya, daya bayan daya mutukar hakan ba ta samu ba to musulmi bai zama mabiyin addnin Allah na hakika ba kuma ba za a ba shi izinin shiga allajana ba. [3]
Da wani yaren bayan da aka aiko manzo Muhammad (s.a.w) kadai addinin da yake karbabbae a wajen allah shi ne na musulunci[4] kuma musuluncin da baya danfare da wilaya (wato yin biyayya da mika wuya da halifanin da Allah ya zaba) ba zai taba zama musulinci na hakika ba kuma ba zai zama cikakken yin Imani da Allah da ranar kiyama ba, ballantana mutum ya shiga cikin aljanna da irin wannan imanin. Don haka kadai hanya ta kai tsaye da mutuum zai shiga Aljannan ta ita ita ce zama dan shi’a tare da tabbatar da cewa zama dan shi’a kadai bai isar ba don ya zama lallai mutum ya zama dan’shi’a na hakika ma’abocin ayyuka na gari don ya zama dan aljanna ko kuma ya zama wanda ya cancani samun cito.
Sai dai raunana (wato jahilai, wadanda aka tauye, mahaukata da yara) wadanda ba su da hanyar ko ba za su iya gano hakaka ba, to zasu saurari hukunci Allah kuma rahamai Allah Ta'ala zata lullubesu sannan su za a fitar da su gada cikin wannan ka’idar. [5]
A nan Zamu anmbaci wasu lamari masu matukar mihimmanci:
- Jahilin da yake tauyayye shi ne wanda gaskiya ba ta iso masa ba kuma kuma bai takaita ba wajen neman gaskiya (Ma’ana tauye shi aka yi amma shi bai tauye kansa ba), ta wannan banagren ba shi da wani laifi, saboda a nan hujjar Allah Ta'ala ba ta hau kansa ba, kuma bisa kaddara cewa hakan daidai ne to matukar hujjar Allah Ta'ala ba ta hau kansa ba, ba zai yiyu mai girma da gaskiya ya rike shi ko ya kama shi da laifi ba. [6]
Don haka zamu iya kasa jahili tauyayye zuwa kaso uku kamar haka:-
- Wanda yake rayuwa a wani yanki da yanayi ya sa gaskiya ba ta isa zuwa gare su ba.
- Masu raunin a tunani; Ana nufin wadanda ba sa iya risker hakikanin yadda al’amura suke, kuma su ne wadanda ba su da kaifin tunani.
- Shi ne wanda yake fama da jahilci murakkabi kuma ya yi yakini kan cewa (A she ne B) kuma wannan yakinin ya samo asali ne ta hanyar dagewarsu. Tare da cewa a hakika (A ba B ba ne).
Amma wanda ya takaita zai kasance cikin azabar Allah shi ne wanda aka bijiro masa da gaskiya kuma da gangan bayan ya san gaskiya ya ki bi ya juya mata baya tare da cewa yana da damar da zai yi riko da ita, sai yayi sakwa-sakwa ya ki ya rike ta.
- Kuma dole ne mu waiwayi cewa Imani da kafirci ba sun doru ne bisa ilimi da tunani zalla ba ne, ballantana ma ayyukan da mutuum ke aikatawa na da tasirin gaske, ta wannan bangaren ne kur’ani ke cewa “sannan karshen makomar wadanda suka aikta munanan ayyuka ta zama karyata wa ga ayoyinmu kuma suka zamo suna yin izgili ga ayoyinmu”. [7]
Dan haka zamu iya cewa: Idan mutuum ya zama bai aikata wasu mumnanan ayyuka ba ko ya kasance bai tasirantu da wasu lamura na siyasa da bangaranci ko kungiyanci ba, ma’ana bai aikata ayyukan da hankali da dabi’a ba zasu karba ba, ya zama ya nisanci wadannan ayyukan, amma sai ya kai ga yakini kan cewa bai gano samuwar Allah Ta'ala ba, kuma bai gane mazhabar gaskiya ba, ko kuma a ce tabbas a hakika ya kai ga yakinin da ya kai shi ga zama kafiri - Allah ya kiyaye - to irin wannan mutumin bisa tsarin adalcin Allah ba ya daga cikin wadanda za a azabtar.
Tabbas wannan bisa asasin hukuncin hankali kenan, amma ya zo a cikin Kur’ani mai girma cewa, lallai wadanda da suka yi kokari kan lamarinmu da sannu zamu nuna musu hanyoyinmu.[8]
- A ruwaoyin da suka zo a musulunci kan yaran da suka bar duniya suna kanana ga yadda ruwayoyin suke kamar haka:-
- Idan iyayen yaran suka zama musulmai:
- A barzahu yaran zasu kasance a karkashin kulawar Annabi Ibrahim ko kuma Sayyida Fadima zasu rika koyar da su har su samu tsarkin huri su kai ga cimma kamala.
- A karkashin tafsirin aya ta 21 surar Daha ya zo cewa za a kai su aljanna wajen iyayensu don su zama masu faranta musu a cikin aljanna}. [9]
- Idan iyayen yaran suka zamo kafirai da munafukai:
- A tafsirin ayar {يطوف عليهم ولدان مخلدون} {yara masu wanzuwa zasu rika kewaya su}[10]. An rawaito cewa ‘ya’yan mushrikai da na kafirai a aljanna zasu zama masu yi wa ‘yan aljanna hidima. Tabbas wannan ba ukuba ba ce a gare su, kuma ba kamar masu yin hidima a duniya suke ba, wadanda ake wulakantawa ko kaskartar wa da makamancin haka ba, balle ma za su zama masu nishadantarwa da farantawa kuma so ado ne.
- Wasu ruwayoyin kuma sun mayar da sanin wannan lamarin ga Allah Ta’ala, suna cewa: “Allah kadai ne ya san abin da zai yi kuma ya san abin da za a mayar da su“.[11]
- Allah Ta’ala zai ba da umarni ta hannun mala’ikan wuta sannan ya ce da mala’ikan ya fito da wasu gungun mutane daga wuta sannan ya sanya wuta ta zama sanyi da aminci a gare su kamar dai yadda ya faru ga annnabi Ibrahim (a.s), kuma daya gungun ba za su shiga ba. kadai wadanda zasu tsira su ne gungun farko. Tabbas mahaukata da wadanda suka zo a lokacin rashin annabci tsakanin zamanin annabawa biyu kuma hujja ba ta hau kansu ba, to su ma sun yi tarayya a cikin wannan hukuncin. [12]
- Wasu daga cikin malaman kalam sun tafi kan cewa, ‘ya’yan mushrikan da kafirai ba za su shiga aljanna ba kuma ba zasu shi ga wuta ba, ballanata na ma za a ajiye su a wani waje da ake kira da a’afari,[13] wanda ba sa cikin azaba kuma ba sa cikin ni’ima. [14]
Marigayi allama Tabata’ie dangane da yara da mahaukata ya kasance yana cewa: abin da kur’ani ya fada dangane da yara da mahaukata dss... maganganu ne da ba za mu iya ciro daidaikun hukunici daga gare su ba cewa su ‘yan wuta ne ko ’yan aljanna ba. Saboda sanin yanayin da mutane ke cikin a lahira ba lamari ne da hankali zai iya gano wa ba, in dai ba cewa zamu yi yin sabo da kuma yin gafara bai iyakantu da sabawa taklifi ba, lalle wasu matakan gafara sun rataya da cututtukan zukata da ruhi wadanda ke shiga cikin zukata su yi shamaki tsakanin ta da mahalincinta. Wadannan jama’ar suna daga cikin mutane na gari, amma saboda raunin hankalinsu ko kuma saboda rashin sa gaba daya sai suka zama takalifi bai hau kansu ba, kuma ba daidai ba ne a ce munana ayyuka ba su yi tasiri a zaukatansu ba kuma zukatansu ba su yi dauda ba har ma an yi musu hijabi daga mahaliccinsu ba. Ballanta ma a wannan janibin daidai suke da sauran mutane. A takaice da wadannan mutanen suna bukatar gusar da wannan daudar da ta yi musu kanta da yaye wannan shamaken dake tsakanin su da Allah Ta'ala don su shiga cikin jindadin samun kusanci a cikin halarori madaukaka na mahalicci, kuma ba wani abu da zai iya gusar musu da wannan shamaki da hijabi sai afuwar Allah Ta'ala madaukaki. Kuma ba abin mamaki ba ne ya zama wannan shi ne abin da wannan aya ke yin nuni gare shi yana dauke da wannan ma’anar:- “Allah Ta'ala zai halicci wuta sannan ya tashi matane sannan sai ya bawa mutane umarni su shiga cikin water, don haka suk wanda ya shiga wuta to zai gan shi a cikin aljannan kuma duk wanda ya ki bin umarnin sai ya shi ga cikin wuta”.[15]
[1] Sarar Buruji aya ta 85.
[2] Sara bakara aya ta 62, hajji aya ta 17, almiazan j 1 shafi na 192-196.
[3] Jigon da ke alaka Shi'a da aljanna, tambaya ta 248.
[4] Suara Ali imrana aya ta 81-91.
[5] Suara nisa’I aya ta 97-99.
[6] “ما کنا معذبين حتي نبعث رسولا” {ba mu kasanc emasu azabtarwa ba har sai mun aika da Manzo}, surar israi aya ta 15. Tabbata abin da ake nufi da maunzaii a nan ba kawai aiko annawada ake nifi ba, ballanta na ma lallae ne ya zama sautin ya isa zuwa mutane, ma’ana idan aka aiko annabawa amma muryar su ba ka isa zuwa gare su ba to hujja ba tahau kansu ba, kuma dalilin hukunta su zai wansu a rataye.
[7] Sura rum, aya ta 10.
[8] “وَ الَّذينَ جاهَدُوا فينا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنا”{Wadanda da suka yi kokari kan lamarin mu da sannun zamu shiyar da su zuwa hanyoyin mu}, surar Ankabut aya ta 69.
[9] Biharul anwar j 5 babi na 13, shafi na 290, da j 6 shafi na 229; amali din saduk, shafi na 269-271.
[10] Sunanr waki’a aya ta 17.
[11] “اللّه اعلم بما كانوا عاملين” {Allah Ta'ala ne mafi sani kan abin da suka kasance suna aikatawa}, “اللّه اعلم بما كانوا فاعلين” {Allah Ta'ala ne ya san abin da sukakasance suna aikatawa}, an cirato daga biharul anwar j 5 shafi na 288- 297 babi na 13.
[12] Buharul anwar j 6 shafi na 292, Hadisi na 14; Biharul anwar j 5 shafi na 295, Hadisi na 22.
[13] Marigayi allama Tabataba’I, ya kawo dalilai da dama kan cewa abin da ake nufi da mazajen A’afari a cikin aya ta 48 sura A’arafi {sai ma’abota a’arafi suka kira wasu mazaje da aka san su da siffofinsu} cewa ba raunanan mutane ba ne, domin samun karin bayani sosai a koma tarjamarAlmizan na tafsirul faeisanci j 8 shafi na 164-156.
[14]Biharul anwar j 5 babi na 13, shafi na 298.
[15] Tarjamar farisanci na almizan j 6 shafi na 535 da 536.