advanced Search
Dubawa
7530
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Shin maganar cewa kowane mutum ana haifarsa da dacensa haka ne kuwa?
SWALI
Shin da ake cewa kowane mutum yayin haihuwarsa ana haifarsa da dacesa ya inganta kuwa? ina neman karin bayani a fadadamin maganar dace.
Amsa a Dunkule

Muna da ruwayoyi da dama da suka yi magana kan ana haifar mutum ne da dacensa, ya zo a ruwayoyi cewa Allah (SW) na fadawa iblis “ban halittarwa dan Adam zuriyarsa ba face sai da na halitta maka misalinta, babu wani daya daga dan Adam face yana tare da shaidanin da ke tare da shi”[1] a wata ruwayar kuma an rawaito daga Manzo (s.a.w) ya ce “babu daya daga cikinku face an wakilta masa makusanci daga aljanu” sai na kusa sukace: harda kai ya rasulllahi? Sai Manzo (s.a.w) ya ce: e harni, sai dai Allah (SW) ya rinjayar dani a kansa yasallama min (ya musulunta) baya umarnina da komai sai alheri.[2] abin da Manzo (s.a.w) ke nufi cikin wannan ruwaya shi ne mutum ya yi kokarin tsare kansa daga wannan abokin wajan kokwantonsa da razaninsa, yadda yake tare damu a rayuwarmu, kuma mu yi kokarin kare kanmu daga tasirinsa da dukkan abin da ya makirta mana duba da abin da Allah (SW) yake yi na turo annabawa da mursalai domin shiyar da dan Adam, alokaci guda shi kuma shaidan da yayansa ba zasu zauna hannu rabbana ba idan mun duba, zasu dinga iya matukar kokarinsu game da duk abin da zai yiwu wajan juyar da dan Adam zuwa bata. Karara wannan a fili yake shedan ya samu nasara kan wasu mutane, su ne wanda suka kau da kai daga ambaton Allah (SW) suka gafala daga gareshi.

Dangane da wannan ne Allah (SW) madaukaki yake fada cikin Kur’ani mai girma “kuma wanda ya makanta wajan hukuncin mai rahama, zamu lullbeshi da shaidani ya zamo abokinsa”[3]

 


[1] Majlisy Muhammad albakir, bihar, bolume 60, page 306, mu’assasatul wafa’a Beirut, Labanon 1404

[2] Majlisy Muhammad albakir, bihar, bolume 60, page 298, mu’assasatul wafa’a Beirut, Labanon 1404

[3] Suratuz zukhruf, aya ta 36.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa