advanced Search
Dubawa
11055
Ranar Isar da Sako: 2006/05/17
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne ma'anar jagorancin malami?
SWALI
Mene ne ma'anar jagorancin malami?
Amsa a Dunkule

Kalmar Wali da larabci tana da ma'ana guda uku: 1-masoyi, 2-aboki, 3-mataimaki. Bayan haka akwai wasu kalmomi kuma da suke nufin; 1-Salladuwa 2-Jagoranci da shugabanci.

"Wilaya" kalma ce da ake amfani da ita da ma'ana biyu a isdilahin fikihu:

1- Wuraren da wanda ake da wilaya kansa ba shi da ikon tafiyar da lamurransa, kamar mamaci, wawa, mahaukaci, yaro, to a nan Kalmar wilaya tana nufin daukar nauyin lura da lamurra. Kuma ma'anaunin yin hakan shi ne shi wanda ake da wilaya kansa ya zama ba zai iya yin lamurransa ba da kansa.

2- Wuraren da wanda ake kula da lamarinsa zai iya tafiyar da lamarinsa, sai dai akwai wasu lamurran da yake bukatar mai kula da lamurransa. A nan wilaya tanan nufin tafiyar da lamurran mutane wato jagorancin siyasa ke nan.

Amsa Dalla-dalla

"Wilaya" a harshen larabci an ciro da daga Kalmar "Walya" ce wacce take da ma'ana guda daya ne da take nufin kusanci[1]. A larabci an yi amfani da Kalmar "walya" da ma'anoni uku ne; 1- so. 2- Kauna. 3- Taimako. Kuma an yi amfani da Kalmar "wilaya" da wadannan ma'anoni da karin wasu bayan hakan da suka hada da[2]: 1- Jagoranci. 2- Iko da tafiyar da hukuma[3].

A harshen farisanci an kawo ma'anoni masu yawa ga wannan kalma kamar aboki, mataimaki, sahibi, mai kiyayewa, wanda yake an sanya shi kula da wani abu, haka nan aka kawo ma'anar tafiyar da hukuma[4].

Yayin da aka yi amfani da Kalmar wilaya ga malami to abin da ake nufi ana amfani da ita ne a kan jagoran hukuma ne, wato shugaba, wanda yake yana da ikon gudanarwa kan lamurran al'umma na hukuma[5].

Wannan yana koma wa zuwa ga tafiyar da lamurran al'umma ne wadanda yake da hakkin tafiyar da lamurransu, kamar dai yadda aka sani cewa shugaban mutane shi ne mai yi  musu hidima[6]. Shi jagora ne kan mutane ba kaya ba ne a kansu.

Ta wani bangaren kuwa a fikihu a nan amfani da wannan kalma ta "wilaya" kamar haka ne:

1- Wuraren da wanda ake da wilaya kansa ba shi da ikon tafiyar da lamurransa, kamar mamaci, wawa, mahaukaci, yaro, to a nan Kalmar wilaya tana nufin daukar nauyin lura da lamurra. Kuma ma'anaunin yin hakan shi ne shi wanda ake da wilaya kansa ya zama ba zai iya yin lamurransa ba da kansa.

2- Wuraren da wanda ake kula da lamarinsa zai iya tafiyar da lamarinsa, sai dai akwai wasu lamurran da yake bukatar mai kula da lamurransa. A nan wilaya tanan nufin tafiyar da lamurran mutane wato jagorancin siyasa ke nan.

"wilaya" a nan tana nufin tafiyar da lamurran al'umma wacce ita ce jagorancin siyasa, kuma duk da cewa Kalmar "wali" tana da wannan ma'ana guda biyu kuma duk za a iya amfani da ita game da jagorancin malami, sai dai a nan muna nufin ma'ana ta biyu ce, domin malami jagoancinsa yana shafar lamari na biyu ne da ya shafi al'umma baki daya wanda ya hada da malamai da sauran 'ya'yan al'umma.

Wannan lamarin bai kasance domin takaituwar al'umma a matsayin al'umma ba ne da wasu suke neman kwatanta jagorancin malami da lamarin kula da lamurran raunana cikin al'umma kamar mamaci ko yaro[7], wannan ya kasance ne domin ita al'umma tana bukatar jagora mai tafiyarwar ne. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Babu makawa ga al'umma su kasance suna da shugaba na gari ne ko fajiri[8]. Wannan wani abu ne da al'umma take bukatarsa matuka

Kuma duk sa'adda aka samu wata al'umam, to dole ne a samu wasu abubuwan da suna bukatar tsari da zai kasance karkashin jagorancin wani mutum daya a matsayin jagora.

Don haka ne malamin da ya kasance a matsayin jagora kan al'umma yake sanya wannan al'ummar kan hanya da shiryarwar musulunci, don hakan ne jagoranci ba komai ba ne sai jagorancin shiriyar addini.

 

Karin bayani:

1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

 


[1]. Makayisul Luga: j 5, s 141. Alkamusul Muheed: s 1732. Almisbahul munir: j 2, s 396. Assihah: j 6, s 2528. Tajul Arus: j 10, s 398.

[2]. Almuntazari: Dirasatun fi wilayatul fakih wa fikhuddaula; j 1, s 55.

[3]. . Alkamusul Muheed: s 1732. Almisbahul munir: j 2, s 396. Tajul Arus: j 10, s 398.

[4]. Muhammad Mu'in, Farhange Farsi, j 4, s 5054 da 5058.

[5]. Mahdi Ha'iri Yazdi, hikmat wa hukumat, s 67 da 177.

[6]. Biharul anwar: majlisi: j 76, s 273. (Shugaban mutane shi ne mai yi musu hidima).

[7]. [7]. Mahdi Ha'iri Yazdi, hikmat wa hukumat, s 67 da 177.

[8]. Nahjul balaga, Subhi Salihi: Khuduba 40, s 82.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Shin matsayin Imamai ya fi na Annabawa?
    11893 Dirayar Hadisi 2017/05/20
    Ruwayoyi masu yawa sun nuna fifikon matsayin ilimin Imamai (a.s) a kan Annabawa, dalili kan wannan maganar shi ne kadaitakar haske da kadaitakar badinin Imamai (a.s) tare da Manzon Allah (s.a.w), saboda shi Manzon Allah (s.a.w) ya fi baki dayan Annabawa, sannan kuma ilimin Imamai an samo ...
  • Don Allah ina so ku yi min bayanin tarihin rayuwar Arkam dan Abi Arkam a takaice?
    4036 صحابه در نگاهی کلی 2017/06/17
    Cikakken sunan Arkam dan Abi’arkam shi ne: Arkam dan Abi’arkam (Abdu Manaf) dan Asad dan Abdullah dan Umar..... dan lu’ayyu bakuraishe, bamahzume,[1] babar sa ita ce Ummayatu ‘yar Abdul Harisu daga kabilar khuza’a ta fito.[2] Yana daga cikin wadanda suka musulunta ...
  • mene ne hadafin halittar dan Adam
    15969 Tsohon Kalam 2012/07/25
    Allah madaukaki shi kansa samuwa ce da ba ta da iya ka ta ko wane bangare kuma y atattara dukkanin wani nau’I na kamala kuma samar da halittu tana nufin koraro da baiwa da ni’ima kuma hakika allah madaukakakin sarki mai yawan kwararo da baiwa ne, kuma ...
  • Yaya aka samu tunanin akidar Rashin addini mai cewa siyasa daban take da addini?
    7160 Sabon Kalam 2012/07/24
    A lokacin samun canjin turan kiristoci sun samu matsala da ta kai su ga cewa addini yana da tawaya, kuma ba zai iya biyan bukatun mutane sababbi ba a fagen siyasa da zaman tare, don haka sai suka kai ga tunanin raba addini da siyasa.
  • Me ya sa ake kashe mai ridda a Musulunci? Shin wannan hukuncin bai sabawa 'yanci akida ba?
    22971 بیشتر بدانیم 2012/09/16
    Yin ridda ita ce bayyana fita daga addini, mafi yawanci tana kasancewa ne tare da bada gudum mawar wasu. Horon mai ridda baya game wanda ya fita daga addini amam ya boye hakan bai bayyana shi ba don kar mutane su sani. A bisa wannan tushen horon ...
  • Meye matsayin jagorancin malami a tsarin siyasar musulunci?
    7049 کلیات 2012/07/24
    A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance ...
  • Mene ne hukuncin sallar mamaci a fikihun Ja’afariyya? Kuma yaya ake yin ta?
    5588 نماز میت 2019/06/15
    Amsar malaman Shi'a game da wannan tambaya yana kamar haka ne: 1. Yin salla ga mamaci musulmi ko yaron da yake da hukuncin musulunci[1] da ya kai shekara shida, wajibi ce[2]. 2. Sallar mamaci kabbarori biyar ce ...
  • Mene ne sharuddan da ke sa wa Rana ta tsarkake kasa da gini?
    7299 بیشتر بدانیم 2012/07/25
    Rana na daya daga masu tsarkakewa kamar yadda ya zo a fikhu, yadda rana ke tsarkake gini da kasa kuwa; ka da a samu tazara tsarkakakkiya tsakanin zahirin (doron) kasa da bayanta (cikinta) ko kuma ginin da hasken ranar zai sauka a kansa kamar iska ko wani ...
  • Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai?
    8275 کرامت انسانی 2012/07/24
    Mutumtakar Mutum A Tare Da Samuwar Sa Take, Ta Yanda A Dukkan Yanayi Ba Zai Yiwu A iya Raba Ta da Shi Ba, Sabanin Shi Musuluncinsa shi Ba a Danfare Da Samuwarsa yake Ba, Sai Dai Zuwa yake Yi, Wato zamu iya Suranta Samuwar Mutum Wanda Ba ...
  • Wane matsayi ne jagorancin malami yake da shi a shi'anci?
    6966 دلائل ولایت فقیه 2012/07/24
    A mahangar Shi'a, jagorancin malami a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), shi ci gaba ne na jagorancin imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma jagorancinsu ci gaba ne na jagorancin manzon Allah (s.a.w). ...

Mafi Dubawa